An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri

  • An hada hankali tsakanin sanatoci 'yan APC mai mulki da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Bola Tinubu
  • Wani rahoto da muka samo ya bayyana ainihin abin da aka tattauna, kuma Tinubu ya magantu a lamarin sanatocin
  • An fara kai ruwa rana da sanatocin jam'iyyar APC tun bayan kammala zaben fidda gwani, wanda ya jawo cece-kuce

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima, ya ce rikicin da ya dabaibaye ‘yan majalisar dattawa na jam’iyyar APC ya shiga rudani, kuma ana ta tattaunawa a kai.

A ranar Lahadi ne Shettima ya jagoranci wasu Sanatoci na jam’iyyar APC wajen ganawa da Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja, inji kafar labarai ta Reuben Abati.

Da yake magana da manema labarai bayan taron, Shettima ya ce Tinubu ya shiga tsakani, ya yi kokarin ya taimaka wajen magance matsalolin da ake fuskanta domin tabbatar da zaman lafiya a tsakanin Sanatoci a jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Abin da ya faru tsakanin Tinubu da Sanatoci
An yi kus-kus: Abin da Bola Tinubu ya shaida wa sanatocin APC a wata ganawar sirri | Hoto: thewillnigeria.com
Asali: UGC

Ya ce sanatocin a shirye suke su yi aiki don ci gaban jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa nan kusa, rahoton The Cable.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shettima ya bayyana abin da ya faru

Shettima ya ce:

"A cikin tsarin da rikice-rikice ke faruwa ba makawa, nuna girma da muke wajen tunkarar rikicin cikin gida, yanayin cikinmu zai nuna yadda za mu iya tafiya a gaba.
“Wadannan Sanatoci kwararrun mutane ne a fannoninsu, wadanda ke da kwakkwaran kima da yawa kuma mun yi imanin shiga tsakani da ya yi (Tinubu) zai yi nisa don guje wa rudani a cikin jam’iyyar.
"Mun samu kyakkyawan yanayin musayar shawarwari tare da 'yan uwanmu daban-daban kuma na yi imanin cewa mun yi nasarar dinke duk wata baraka da ke tafe."

Kwanan nan ne Sanatocin APC da dama suka sauya sheka zuwa wasu jam’iyyun siyasa bayan kammala zaben fidda gwani na APC.

Kara karanta wannan

Jigon APC: Sanatocin Mu 22 Suna Barazanar Komawa Jam'iyyar PDP, Dole Mu Dauki Mataki

Wadanda suka sauya shekan sun bayar da misali da yadda ake zargin su da nuna wariya, rashin bin tsarin dimokuradiyya na cikin gida, da kuma rashin adalci a wani bangare na dalilan da suka sa suka tsallake jam'iyyar.

Wasu daga cikin Sanatocin da suka sauya sheka na neman a sake zabensu amma sun sha kaye a zaben fidda gwanin jam'iyyar da aka kammala watan jiya.

Jigon siyasa: Kada Igbo su bata kuri'a wajen zaban Atiku, su zabi Tinubu saboda wani dalili

A wani labarin, Amb Ginika Tor ta yi kira ga al’ummar yankin kudu maso gabas da kada su yi kuskuren zaben jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa na 2023 mai zuwa.

Wakiliyar ta jihar Enugu a hukumar da’a ta tarayya ta ce jam’iyyar PDP ba ta cancanci kuri’un kabilun Igbo ba, saboda kin amincewar jam’iyyar na ba da tikitin takarar shugaban kasa a yankin kudu maso gabas, inji rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Ta ce a maimakon goyon bayan Atiku tare da kada masa kuri'u, ya kamata dan takarar jam'iyyar APC, Sanata Bola Ahmed Tinubu ya shahara ya kuma mamaye kuri'un yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel