Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

Karin Bayani: Adamu Da Sanatocin APC Sunyi Taro, An Dauki Matakan Dakile Ficewar Mambobin Jam'iyyar

  • Sanata Abdullahi Adamu, Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress, APC, na kasa ya yi taro da sanatocin APC
  • Adamu da Sanatocin sun tattauna kan batun ficewa daga jam'iyyar mai mulki a kasa da mambobin ta ke yi a baya-bayan nan
  • Shugaban na APC ya ce sauya shekan ba sabon abu bane musamman a shekarar da ake tunkarar zabe amma dai sun damu kuma za su dauki matakai

FCT, Abuja - Shugaban jam'iyyar All Progressive Congress, APC, na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, a halin yanzu yana ganawar sirri da sanatocin jam'iyyar, rahoton The Punch.

Adamu ya isa hedkwatar jam'iyyar ta APC da ke Abuja misalin karfe 2 da wasu mintuna sannan ya wuce ofishin shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, suka gana na dan mintuna kafin ya wuce wurin babban taron.

Kara karanta wannan

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

Shugaban APC Abdullahi Adamu.
Shugaban APC, Adamu, Ya Na Gannawar Sirri Da Sanatoci. Hoto: @MobilePunch.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tunda farko, Lawan yayin karanto wasika mai dauke da sa hannun mataimakin marasa rinjaye na majalisa, Ajayi Borofice, ya sanar da cewa za a yi taron ne misalin karfe biyu a harabar majalisar.

The Punch ta rahoto cewa adadin sanatocin jam'iyyar APC ya rage ya koma 62 bayan da wasu yan majalisun suka rika ficewa musamman wadanda suka gaza samun tikitin sake yin takarar kujerunsu a 2023.

Sanatoci biyu daga Bauchi da Imo sun sanar da murabus dinsu daga APC da PDP yayin zaman majalisar.

Sanatocin sune Sanata Dauda Jika mai wakiltar Bauchi Central da aka zaba karkashin APC; da Sanata Ezenwa Francis wanda aka zaba karkashin PDP.

Jam'iyyu marasa rinjaye a majalisa su biyar ne kawo yanzu, yau Laraba 22 ga watan Yunin 2022.

Kara karanta wannan

PDP ta ragu: Sanatan PDP ya sauya sheka, ya bi sahun Peter Obi a jam'iyyar Labour

Sune PDP, YPP. APGA, NNPP da LP.

Mun damu da ficewarsu sanatocin APC - Adamu

Da ya ke yi wa manema labarai jawabi bayan taron sirrin, Adamu ya ce APC ta damu da yadda sanatocinta ke barin jam'iyyar.

Yayin da ya ke nuna damuwarsa, Adamu ya lura cewa (sauya shekan) ba sabon abu bane musamman a shekarar da ake tunkarar zabe amma dai duk da haka jam'iyyar da shugabanninta sun damu.

Ya ce:

"Taron mu da sanatoci ta yi albarka. Batun sauya sheka bai mana dadi ba amma hakan dama na faruwa a kakar zabe kuma yana faruwa a wasu jam'iyyun da ba APC kadai ba.
"A kowanne shekarar zabe, irin wannan abin na daukan hankalin masu ruwa da tsaki, Najeriya da APC ba su tsira ba. Ban damu da abin da ke faruwa a wasu jam'iyyu ba, hankali na ya karkata ne a APC. Amma dai mun san ba APC kadai abin ke faruwa ba, yana faruwa a wasu jam'iyyun. Amma saboda mune jam'iyya mai mulki, an fi haskaka abin da ke faruwa da mu."

Kara karanta wannan

AbdulMumini Jibrin ya daura hoton Kwankwaso ya 'badda kama, tambar Obama

Adamu ya ce ba shi da tabbas idan batun sauya shekar zai tsaya amma ya gana da takwarorinsa a majalisa kuma yana fatan za a yi nasara.

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel