Gwamna Wike ya fadi dalilin da ya sa 'Dan takaran NNPP, Kwankwaso ya ziyarce shi a gida

Gwamna Wike ya fadi dalilin da ya sa 'Dan takaran NNPP, Kwankwaso ya ziyarce shi a gida

  • Nyesom Wike ya yi karin haske game da haduwar da aka ga ya yi da mutanen Rabiu Kwankwaso
  • Gwamnan na jihar Ribas ya bayyana cewa an yi tattauna mai zurfi da ya hadu da ‘dan takaran NNPP
  • Kwankwaso ya samu kyakkyawar a wajen Wike wanda ya gana da Peter Obi duk a cikin makon nan

Rivers - Bayan fiye da sa’a 24, Nyesom Wike ya cire mutane daga duhu, a game da ganawar sirrin da ya yi da ‘dan takarar NNPP, Rabiu Musa Kwakwanso.

Jaridar Reuben Abati ta rahoto Mai girma Gwamna Nyesom Wike yana magana a game da haduwarsa da tsohon gwamnan na jihar Kano a gidansa.

Sanata Rabiu Kwakwanso wanda yake takarar shugaban kasa a jam’iyyar hamayya ta NNPP ya yi takakkiya har zuwa Fatakwal domin ya zauna da Wike.

Kara karanta wannan

Yau Kwankwaso zai yi zama na musamman da Nyesom Wike a kan shirin zaben 2023

Kamar yadda mu ka samu rahoto, da yake bayani, Nyesom Wike ya ce sun tattauna a kan muhimman abubuwa masu zurfi da fitaccen ‘dan siyasar.

Allah kadai ya san karatun kurma

Gwamnan na Ribas ya nuna maganar zuciya ta dauko Kwankwaso daga birnin tarayya Abuja, ta kawo shi garin Fatakwal domin su sa labule a ranar Juma’a.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Wike wanda ya sha kashi wajen zama ‘dan takarar shugaban kasa a PDP ya nuna maganarsu da Kwankwaso ta yi zurfi fiye da yadda mutane su ke tunani.

Kwankwaso da Gwamna Wike
Nyesom Wike da Rabiu Kwankwaso a Fatakwal Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

A game da diddikin abin da tattaunawarsu ta kunsa, Wike bai yi wa jama’a wani karin haske ba. An yi wannan haduwar ne ba a gaban manema labarai ba.

A wasu rahotannin, an ji cewa ana ganin ziyarar ta kunshi gayyatar hadin-kai tsakanin Wike wanda yake PDP da NNPP da sauran sauran jam’iyyun hamayya.

Kara karanta wannan

2023: Zawarcin da APC, Peter Obi su ke yi wa Wike ya fara kada hantar jagororin PDP

Wasu kuma su na ganin Kwankwaso yana neman wanda zai zama masa 'dan takarar mataimakin shugaban kasa ne idan haduwarsa da Peter Obi ta gagara.

An rabu faram-faram

Mu na da labari cewa an ga Wike da Kwakwanso su na farin ciki bayan Gwamnan ya tura tawaga ta musamman ta tarbo babban 'dan siyasar daga filin jirgin sama.

Kafin ‘dan takaran shugaban kasar ya bar Fatakwal, an gan shi da tsohon gwamnan Ekiti, Ayo Fayose wanda yana cikin na kusa da Wike yana yi masa sallama.

Kwankwaso wanda rabonsa da yin magana a shafin Twitter kusan kwanaki 20 kenan, ya fito a jiya, yana mai yi wa Gwamnan godiya da irin tarbar da ya yi masa.

Ga Madugu ga Wike

Tun da rana ku ka samu labari cewa bayan Gwamna David Umahi da Peter Obi sun sa labule da Gwamnan jihar Ribas, Rabiu Kwankwaso zai zauna da shi a gida.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Ana tunanin haduwar jagoran na jam'iyyar adawa ta PDP da Madugun na Kwankwasiyya ba za ta rasa nasaba da neman abokin takararsa a jam’iyyar NNPP ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel