An sake samun Gwamnan APC da ya yi wa Tinubu alkawarin kuri’un Jiharsa a zaben 2023

An sake samun Gwamnan APC da ya yi wa Tinubu alkawarin kuri’un Jiharsa a zaben 2023

  • Ben Ayade ya yi alkawarin zai yi wa Asiwaju Bola Tinubu da Jam’iyyarsu ta APC aiki a zaben 2023
  • Kashi 100% na kuri’un mutanen jihar Kuros Riba za su tafi akwatin APC ne a cewar Farfesa Ayade
  • Gwamnan ya ce ba zai fasa yi wa Tinubu aiki ba duk da shi ma ya nemi yin takarar shugaban kasa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Cross River - Ben Ayade wanda shi ne gwamnan jihar Kuros Riba, ya sha alwashin ganin jam’iyyar APC mai mulki ta samu nasara a zaben shugaban kasa.

Punch ta rahoto Farfesa Ben Ayade yana mai cewa zai yi bakin kokarinsa na ganin ‘dan takaran APC, Asiwaju Bola Tinubu ya samu 100% na kuri’un jihar a 2023.

Da yake jawabi a ranar Talata, 21 ga watan Yuni 2022, Ayade yace zai yi wa Bola Tinubu aiki, ba tare da la’akari da yadda zaben neman takara a APC ya kasance ba.

Kara karanta wannan

Na lura ana neman yi mani taron dangi ne, Bola Tinubu ya fadi dalilin yi wa Buhari gori

Ben Ayade yana cikin wadanda suka shiga zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC, amma shi da sauran ‘yan siyasa 12 suka sha kashi a hannun jigon APC, Tinubu.

Ayade ya dawo daga Sifen

Kamar yadda mu ka samu labari, Ayade ya yi wa manema labarai jawabi ne a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Margaret Ekpo da ke garin Kalaba a jiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnan yake cewa ya godewa Ubangiji da ya samu damar jarraba sa’a a neman takarar shugaban kasa, ya kuma ji dadin abin da ake ta fada a game da shi.

Ayade da Tinubu
Ben Ayade tare da su Bola Tinubu Hoto: www.ripplesnigeria.com
Asali: UGC

“Shakka babu, mutane sun gamsu cewa zan iya kawowa kasar nan cigaba, amma sai dai kawai lokaci na bai yi ba tukun.”
“Yanzu lokacin wani ne dabam, kuma ina yi wa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu murna na samun takara a jam’iyyarmu.”

Kara karanta wannan

Shugaban kamfe ya kyankyasa inda Abokin takarar Tinubu zai fito daga Jam’iyyar APC

“Kamar yadda tsarin jam’iyyarmu ta ke, za mu hadu gaba dayanmu, mu yi aiki domin mu ba shi nasara a zaben 2023.”
“Kuros Riba za ta tabbatar kashi 100% na kuri’anta sun tafi ne wajen ‘dan takararmu na shugaban kasa (Bola Tinubu).”

- Ben Ayade

PM news ta ce Farfesan ya yi bayanin abin da ya kai shi kasar Sifen inda ya tattauna da wasu kamfanonin jiragen sama domin farfado da filin jirgin garin Kalaba.

Atiku zai lallabi su Wike

A safiyar Laraba aka samu labari cewa wani kwamiti na manyan ‘yan jam’iyyar PDP da aka kafa, zai bi su Nyesom Wike har gida domin shawo kansu kafin zaben 2023.

Bisa dukkan alamu, 'Dan takaran PDP, Atiku Abubakar zai so ya dinke duk wata baraka ta yadda zai iya doke Bola Tinubu da sauran ‘Yan takara a zaben shugaban Kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel