2023: Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake shiga tseren shugaban kasa, an nemi ya hade da Kwankwaso

2023: Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake shiga tseren shugaban kasa, an nemi ya hade da Kwankwaso

  • An rahoto cewa mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar Kwankwaso
  • Wasu makusantan Osinbajo tare da hadin gwiwar wasu manyan yan siyasa daga arewa ne suke jagorantar wannan kiran
  • Lissafin masu yunkurin wannan hadi shine cewa addini zai taka muhimmiyar rawa wajen zabar magajin shugaban kasa Buhari a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Rahotanni sun kawo cewa ana kulla-kulla don hada kawance tsakanin jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da sansanin mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kokarin ganin ya dawo tseren shugaban kasa na 2023.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa majiyoyi a sansanonin biyu sun dage cewa akwai shawarwari masu karfi da ke gudana dangane da yiwuwar samun tikitin Osinbajo/Kwankwaso a karkashin inuwar jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Jami'in INEC: Kuskure ne Ayyana Machina Matsayin 'Dan Takarar Sanatan Yobe ta Arewa a APC

Osinbajo and Kwankwaso
2023: Osinbajo na fuskantar matsin lamba don sake shiga tseren shugaban kasa, an nemi ya hade da Kwankwaso Hoto: Daily Post
Asali: UGC

An nakalto daya daga cikin majoyoyin na cewa:

“Daya daga cikin dalilan da suka sanya ake kokarin samar da tikitin Osinbajo/Kwankwaso shine bukatar cika muradin jama’a na samar da wani nau’in shugabanci na daban, wanda shine abun da mataimakin shugaban kasar ya zo yiwa yan Najeriya wakilcinsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A daya bangaren kuma, Kwankwaso an san shi ne a matsayin kwararren dan siyasa a yankin arewa maso yamma wanda cikin sauki zai iya cike gurbin mataimakin shugaban kasa.”

A cewar majiyoyin, wasu hadiman mataimakin shugaban kasar tare da hadin gwiwar wasu manyan yan siyasar arewa ne suke jagorantar wannan yunkurin.

A cewar majiyoyin, shirin shine maye gurbin Kwankwaso, wanda jam’iyyar ta rigada ta gabatar da sunansa a matsayin dan takararta na shugaban kasa, ta hanyar amfani da kafar sauyi wanda ke bude har zuwa watan Agusta.

Kara karanta wannan

2023: A Karshe, Igbo Sun Bayyana Wanda Za Su Zaba Tsakanin Tsakanin Tinubu, Atiku Da Obi

Koda dai wasu na kusa da mataimakin shugaban kasar sun yi watsi da rahoton, inda suka bayyana shi a matsayin hasashe kawai, majiyoyin sun magantu a kan yiwuwar samar da tikitin Osinbajo/Kwankwaso a karkashin inuwar NNPP.

A cewar daya daga cikin majiyoyin, lissafin shine cewa addini zai taka gagarumin rawar gani wajen zabar wanda zai gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023.

Sannan cewa cike gurbin da mataimakin shugaban kasar wanda ya kasance kiristan kudu, zai tabbatar da ganin cewa an ba arewa damar zabar Musulmi a matsayin abokin takararsa kuma saboda haka,. Kwankwaso ya fi dacewa da zama mataimakin Osinbajo.

Masu neman takarar gwamna 3 sun sauya sheka daga APC zuwa PDP a jihar Sokoto

A wani labarin kuma, mun ji cewa akalla masu neman takarar kujerar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a zaben fidda gwanin da aka yi kwanan nan ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Zunuban Ike Ekweremadu: Manyan rigingimu 4 da tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya fada ciki

Daga cikin wadanda suka sauya sheka daga APC zuwa PDP sun hada da wani dan majalisar wakilai, Hon Abdullahi Balarabe Salame, jaridar Punch ta rahoto.

Salame wanda ke wakiltan mazabar Ilella/Gwadabawaa majalisar dokokin tarayya, ya kasance dan majalisa sau uku, sannan ya yi zango biyu a majalisar dokokin jiha, inda ya rike mukamin kakakin majalisa da kuma mukaddashin gwamnan jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel