Yau Kwankwaso zai yi zama na musamman da Nyesom Wike a kan shirin zaben 2023

Yau Kwankwaso zai yi zama na musamman da Nyesom Wike a kan shirin zaben 2023

  • ‘Dan takarar jam’iyyar hamayya ta NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai yi zama da Nyesom Wike
  • Da alama Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana neman wanda zai zama abokin takararsa a 2023
  • Haduwar Kwankwaso za ta zo ne sa’anni kadan bayan Peter Obi ya gana da Gwamnan a gidansa

Rivers - Mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso zai hadu da Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.

Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman cewa Rabiu Musa Kwankwaso yana shirin sa labule da jagoran na jam’iyyar PDP.

‘Dan takaran shugaban kasar zai gana da Gwamnan ne a lokacin da yake neman wanda zai yi masa takarar mataimakin shugabancin kasa.

A halin yanzu Sanata Kwankwaso da jam’iyyarsa ta NNPP su na tsakiyar tattaunawa da ‘dan takarar jam’iyyar LP watau Mista Peter Obi.

Kara karanta wannan

2023: Zawarcin da APC, Peter Obi su ke yi wa Wike ya fara kada hantar jagororin PDP

An samu tasgaro a tattaunawar yayin da kowane bangare ya dage a kan cewa shi za a ba tikitin shugaban kasa idan jam’iyyun sun hade.

Rahoton ya ce watakila tsohon Gwamnan na Kano zai zauna da Wike ne domin neman wata mafitar idan har ya gaza shawo kan Obi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwankwaso
Nyesom Wike a gidan Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @SaifullahiHon
Asali: Twitter

Za a gana da Fatakwal

Hadiman Kwankwaso sun tabbatar da cewa da kimanin karfe 2:30 na ranar Juma’a, 24 ga watan Yuni 2022 za ayi wannan zama a Fatakwal.

Legit.ng za ta tuna, gabanin ficewar ‘dan takaran na NNPP daga PDP, Mai girma Wike ya hadu da shi a gidansa da ke birnin tarayya Abuja.

Ko bayan babban ‘dan siyasar na Arewacin Najeriya ya sauya-sheka zuwa NNPP, dangantakarsa da Gwamnan na jihar Ribas ba ta cabe ba.

‘Ya ‘yan jam’iyyar hamayya ta PDP na reshen jihar Kano duk sun zabi Wike ne a lokacin zaben fitar da gwanin zama shugaban kasa a PDP.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da Peter Obi su na tsere da INEC domin yi wa PDP da APC taron dangi mai-karfi

Har yanzu NNPP ba ta tsaida takamaimen ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa ba, babu mamaki Wike yana cikin lissafin da ake yi.

Wike ya tada hankalin PDP

Ku na da labari cewa shugabannin PDP da Atiku Abubakar sun fara jin tsoron Nyesom Wike ya tsallaka zuwa wata jam’iyyar kafin zabe.

Da alama Nyesom Wike ya sa ran Atiku Abubakar zai dauke shi a matsayin abokin takara a PDP, don haka aka tura kwamiti ya ba shi hakuri.

Asali: Legit.ng

Online view pixel