Mutanen Mazabar Sanatan Kudu Sun Juya Masa Baya Saboda Yana Goyon Bayan Tinubu Ya Zabi Abokin Takara Musulmi

Mutanen Mazabar Sanatan Kudu Sun Juya Masa Baya Saboda Yana Goyon Bayan Tinubu Ya Zabi Abokin Takara Musulmi

  • Sanata Orji Kalu ya shiga matsala saboda kalaman da ya furta na shawartar Bola Ahmed Tinubu ya zabi abokin takara musulmi idan yana son cin zaben 2023
  • Bulaliyar na Majalisar ya bayyana cewa kuskure ne Tinubu kasancewarsa musulmi mara rinjaye daga kudu ya zabi kirista wanda shima mara rinaye ne a arewa
  • Wannan kalaman sun janyo wa Kalu martani zafafa daga sarakuna da masu fada a ji daga mazabarsa suna mai cewa sun raba jiha da shi kuma ya janye maganar ya nemi afuwarsu

Abia - Mutane daga mazabar bulaliyar majalisar tarayya kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Kalu, sun raba jiha da shi, saboda ya shawarci dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu ya zabi musulmi a matsayin abokin takararsa a 2023, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana kishin-kishin, Tinubu ya nuna wanda yake so ya zama Mataimakinsa a zaben 2023

Kalu, wanda ya jadada cewa babu matsala idan musulmi da musulmi sun yi takara, ya ce kuskure ne Tinubu, wanda musulmi ne cikin marasa rinjaye a kudu ya zabi kirista daga arewa wanda shima yana cikin marasa rinjaye a matsayin mataimakinsa.

Sanata Orji Kalu Mai Wakiltar Abia North.
Orji Kalu Ya Shiga Matsala Saboda Goyon Bayan Tikitin Musulmi Da Musulmi, Mutanen Yakinsa Sun Juya Masa Baya. Hoto: @VanguardNGR.
Asali: Twitter

Martanin Sarakuna na mazabar Abia North

A martaninsa, Basaraken garin Abiriba, Eze Kalu Kalu Ogbu (Enachoken) ya ce abin da tsohon gwamnan ya fada ba su gamsu da shi ba kuma bai bada ma'ana ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce zaben addini guda daya wurin takara a Najeriya ba zai bada nasara ba don haka duk wanda ke bada wannan shawarar, kamata ya yi a yi watsi da shi.

"Abin ya daure mana kai. Bana tsammanin ya fadi hakan amma idan ya fada, bai yi magana a madadin Abia ta Arewa ba, bai yi magana a madadin Ndigbo ba don maganar bada bata ma'ana ba. Bata dace ba kwata-kwata."

Kara karanta wannan

Mataimakin shugaban kasa: Daga karshe Tinubu ya fayyace gaskiyar lamari kan tikitin Musulmi da Musulmi

Kazalika, Jigon PDP a Abia North, Dr Isaac Nkole, ya ce Kalu ya dade da rasa izzarsa na siyasa don haka yana neman samun shiga ne a fadar Tinubu.

Da ya ke magana kan batun, tsohon shugaban kwamitin sarakuna na Oriendu, Mai Girma Eze Philip Ajomuiwe, ya ce ra'ayin tsohon gwamnan kan batun bai dace ba kuma yana iya tada zaune tsaye.

Ya bukaci ya janye maganar, wanda a cewarsa bata dace da sanata kamansa ba.

Basaraken ya ce Kalu abokinsa ne kuma ya nuna bacin ransa kan maganar, yana mai cewa zai kira shi ya fada masa yadda ya ji game da maganan.

"Ban san kalaman da zan yi amfani da su don kwatanta abin da Kalu ya yi ba. Ya za ka ce hakan za ta faru a Najeriya? Tikitin musulmi da musulmi zai janyo tada zaune tsaye. Ba za mu iya bada shawarar a yi kirista da kirista ba. Dole a samu daidaito saboda Najeriya ta damu da addini."

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Ekiti 2022: 'Idan Ba Kuri'a, Ba Kudi', Bidiyon Tinubu Yana Yi Wa Masu Zabe Ba'a a Wurin Kamfen

A wani rahoton, Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a zaben 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya bukaci al'ummar Jihar Ekiti su fito su yi zabe idan ba hakan ba ba za a biya su ba.

Tinubu, wanda ya ziyarci a Jihar Ekiti a ranar Talata ya furta hakan ne wurin yakin neman zabe na dan takarar gwamna na jam'iyyar, Biodun Oyebanji gabanin zaben da ake shirin yi ranar Asabar 18 ga watan Yunin 2022.

Ya kuma kambama kansa cewa bai taba fadi zabe ba a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel