Fasto: A siyasa babu batun addini, ba komai bane don APC ta yi tikitin Musulmi da Musulmi
- Babban malamin addinin Kiristanci, Bishop Silas Eke, ya goyi bayan Sanata Orji Kalu a kan tikitin Musulmi da Musulmi da APC ke shirin yi a babban zaben 2023
- Bishop Eke ya bayyana cewa ba laifi bane don an tsayar da Musulmi da Musulmi domin siyasa babu ruwanta da addini
- Da yake cewa Kalu bai ce APC ta mayar da Najeriya kasar Musulunci ba, malamin ya ce babu yadda za a yi jam'iyyar ta lashe zabe da Kiristan arewa a matsayin mataimakin Tinubu
Abia - Bishop Silas Eke na cocin Kingly People’s Assembly ya goyi bayan mai tsawatarwa a majalisar dattawa, Orji Kalu, kan matsayarsa na marawa tikitin Musulmi da Musulmi baya a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin zaben 2023.
Bishop Eke ya kuma bayyana cewa sanata Kalu bai cewa APC ta mayar da Najeriya kasar Musulunci ba.
Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a yammacin ranar Laraba a Umuahia, Bishop Eke ya marawa Sanata Kalu baya kan goyon bayan tikitin Musulmi da Musulmi, Nigerian Tribune ta rahoto.
A cewarsa:
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Babu laifi cikin abun da ya fadi. Jam’iyyar na damar yin nasara da tikitin Musulmi da Musulmi. Ban ji Kalu yana fada ma APC ta Musuluntar Najeriya ba. Ina ganin yana kan hanya.”
Babban faston ya kara da cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta iya lashe zaben shugaban kasa na 2023 ba da kirista marasa rinjaye a yankin arewacin Najeriya a matsayin mataimakin Tinubu.
Ya kuma bukaci wadanda ke adawa da kudirin shugabancin tsohon gwamnan na jihar Lagas, Bola Ahmed Tinubu da kada su soki Kalu kan kokarinsa na zama jajairtaccen dan jam’iyya.
Malamin addinin ya bayyana cewa Kalu ya yi magana ne a matsayin jajirtaccen dan APC mara son kai, New Telegraph ta rahoto.
Ya kara da cewa:
“Kada mu manta cewa sanata Orji Uzor Kalu dan APC ne da ya fito daga yankin da jam’iyyar bata da farin jini sosai.
“Yawancin masu sukar jawabinsa suna yi ne saboda son zuciya. Amma a iya sanina, babu wani abu mai kama da raunin zuciya a siyasa.
“Jam’iyyarsa na son yin nasara kamar yadda PDP ke son yin nasara, don haka ina ganin kawai ya bayyana dabarar jam’iyyar ne ga yan Najeriya wadanda basa adawa da kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Yana bisa kan tsari. Masu adawa da shi kawai suna jin haushi ne saboda jam’iyyar da dan takararta.”
A kwanakin baya ne dai Sanata Orji Uzor Kalu ya dage cewa babu laifi idan jam'iyyar APC ta yanke shawarar fitar da yan takara musulmi da musulmi a zaben shugaban kasa na 2023.
Idan Tinubu bai zabi mataimaki Musulmi ba, da wuya APC taci zabe: Orji Kalu
A baya mun ji cewa mai tsawatarwa a majalisar dattijan tarayya, Ori Uzor Kalu, ya bayyana cewa da kamar wuya jam'iyyar All Progressives Congress APC ta lashe zaben shugaban kasa idan bata dauki mataimaki Musulmi daga Arewa ba.
Kalu ya ce yanzu ya zama wajibi Tinubu ya dauki Musulmi muddin yana son lashe zabe a 2023.
Dan siyasan yace jam'iyyar APC na tsaka mai wuya yanzu.
Asali: Legit.ng