Idan Tinubu bai zabi mataimaki Musulmi ba, da wuya APC taci zabe: Orji Kalu

Idan Tinubu bai zabi mataimaki Musulmi ba, da wuya APC taci zabe: Orji Kalu

Mai tsawatarwa a majalisar dattijan tarayya, Ori Uzor Kalu, ya bayyana cewa da kamar wuya jam'iyyar All Progressives Congress APC ta lashe zaben shugaban kasa idan bata dauki mataimaki Musulmi daga Arewa ba.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kalu ya ce yanzu ya zama wajibi Tinubu ya dauki Musulmi muddin yana son lashe zabe a 2023.

Dan siyasan yace jam'iyyar APC na tsaka mai wuya yanzu.

Ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayinda yake hira da manema labarai a majalisar dokokin tarayya Abuja, rahoton ChannelsTV.

Yace:

"Idan bamu dauki Musulmi mataimaki ba, mun shiga uku."
"Da kamar wuya mu lashe zabe saboda abu zabi daya da Ahmed Tinubu ke da shi shine kawai ya dauki Musulmi."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kano: Majalisar Dokoki Amince Ganduje Ya Ciyo Bashin Naira Biliyan 10

"Mun shiga wani hali da ba zamu iya zaben marasa rinjaye biyu ba- Tinubu Musulmi ne daga kudu idan Kirista ke da rinjaye, sannan kuma daukan Kirista mara rinjaye daga Arewa. Wannan shine gaskiyar lamari."
"Amma fa wannan ra'ayina ne."

Hira da manema labarai
Idan Tinubu bai zabi mataimaki Musulmi ba, da wuya APC taci zabe: Orji Kalu Hoto: Press Conference
Asali: Facebook

Asali: Legit.ng

Online view pixel