Rashin tunani ne Tinubu ya zabi Musulmi matsayin mataimakinsa: Hedkwatar Cocin Katolika

Rashin tunani ne Tinubu ya zabi Musulmi matsayin mataimakinsa: Hedkwatar Cocin Katolika

  • Darikun addinin Kirista daban-daban na cigaba da gargadin jam'iyyun APC da PDP kada su zabi Musulmi mataimaki
  • Darikar Katolika a nata jawabin ta bayyana cewa zaben Musulmi shugaba kuma Musulmi mataimaki rashin tunani ne
  • Yau ko gobe jam'iyyar APC, PDP, LP a NNP zasu sanar da wanda zai yiwa yan takararsu mataimaki

Abuja - Hedkwatar Cocin Katolika a Najeriya ta bayyana rashin amincewarta da yunkurin Musulmi da Musulmi suyi shugaban kasa da mataimaki a zaben 2023.

Cocin ta bayyana matsayarta ranar Talata ne a jawabin da Sakatare Janar dinta, Zacharia Nyantiso Samjumi, ya fitar, rahoton TheCable.

A jawabin, cocin tace wajibi ne dukkan jam'iyyun siyasa su fahimci cewa hadin kan Najeriya ya dogara ne kan daidaito tsakanin addinai.

Jawabin yace ko lokacin mulkin Soja, da tsarin Musulmi-Kirista akayi amfani.

Kara karanta wannan

Yau ko gobe Juma'a: Ganduje, Shettima, da mutum biyu da ake sa ran Tinubu zai zaba, Majiya

Catholics
Rashin tunani ne Tinubu ya zabi Musulmi matsayin mataimakinsa: Hedkwatar Cocin Katolika Hoto: Presidency

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yace:

"Misali, an yi mulkin Murtala-Obasanjo, Obasanjo-Yar'adua, Babangida-Ebitu Ukiwe, Abacha – Diya. Hakazalika shugabannin hukumomi daban-daban irinsu Kwastam, Immigration, dss."
"Lokacin mulkin Sojan Buhari kadai aka samu Musulmi da Musulmi. Hakazalika lokacin zaben Abiola-Kingibe."
Cocin tace asali bai kamata wannan ya zama matsala ba idan kan yan Najeriya a hade yake, amma kan yan Najeriya yanzu ya rabu kashi-kashi."
"Dubi ga rabuwar kai dake tsakanin yan kasar nan, Tikitin Musulmi-Musulmi ba karamin rashin tunani zai zama ba. "
"Dubi ga abinda ya faru a Kaduna, da alamun irin wahalan da Kiristocin kudancin Kaduna suka sha zai sake faruwa."

Cocin ta karkare jawabinta da kira ga jam'iyyun siyasa kada su sake su zabi abokin takara Musulmi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel