Ka zabi daya: Shehu Sani ya tada kura a intanet, ya nemi Osinbajo ya zabi Atiki ko Tinubu

Ka zabi daya: Shehu Sani ya tada kura a intanet, ya nemi Osinbajo ya zabi Atiki ko Tinubu

  • Sanata Shehu Sani ya jawo cece-kuce a shafin Twitter bayan da ya bayyana abin da ke cikin sakon WhatsApp da ya tura wa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
  • Sani, wanda tsohon dan majalisar tarayya ne, ya ce ya tambayi Obasanjo ya bayyana waye dan takarar shugaban kasa da ya fi so tsakanin Atiku na PDP da Tinubu na APC
  • Yayin da Sanatan ya ce yana jiran amsar tsohon shugaban kasar, 'yan Najeriya da dama a dandalin sada zumunta sun mayar da martani daban-daban kan tambayar da ya yi

Najeriya - Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta takwas, Shehu Sani, ya ce ya tambayi tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya zabi dan takarar shugaban kasa kafin zuwan 2023.

Kara karanta wannan

Takarar Musulmi da musulmi: Ana yiwa Tinubu zagon kasa ne, in ji wani fasto

Sani a wani sako da Legit.ng ta gani a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, 13 ga watan Yuni, ya ce ya roki Obasanjo ta Whatsapp da ya zabi dan takara tsakanin tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da Bola Ahmed Tinubu.

Shehu Sani ya tura wasika ga Obasanjo, ya zabi Atiku ko Tinubu
Ka zabi daya: Shehu Sani ya tada kura a intanet, ya nemi Osinbajo ya zabi Atiki ko Tinubu | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Tsohon sanatan ya kara da cewa zai yi wa mabiyansa bayani a dandalin sada zumunta idan tsohon shugaban kasar ya amsa masa.

Atiku da Tinubu su ne ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP da APC a zaben 2023 mai zuwa, jam'iyyu biyu mafi tasiri a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Na aika da sakon WhatsApp ga Baba Obasanjo ya zaba daga cikin jiga-jigan nan biyu. Idan ya amsa, zan sanar da ku. Idan ba ku ji ta bakina ba, hakan na nufin har yanzu bai ba da amsa ba."

Kara karanta wannan

2023: Dalilin da Yasa APC ta Zabi Tinubu, El-Rufai Ya yi Bayani Mai Bada Mamaki

Atiku ko Tinubu: 'Yan Najeriya sun mayar da martani

Legit.ng ta lura cewa sakon da Sani ya wallafa a shafinsa na Twitter ya jawo martani daban-daban daga 'yan Najeriya a shafin, ga kadan daga ciki:

@bodyglamz, yayi sharhi da cewa:

"Zai amsa da misali mai kama hankali."

@official_amicus ya ce:

"Duk wanda ya zaba ba zai taba hana ni goyon bayan Peter Obi ba, wannan bai shafe ni ba."

@tweetJudon, ya ce:

"Kana so OBJ ya zaba tsakanin jahannama da wuta ne."

@Victorbajju_30, ya ce:

“Bai kamata Obasanjo ya kara yanke hukunci kan makomar Najeriya ba, mun wuce lokacin da dattawan kasa za ke su fada mana dan takarar da suke so.
"Aminci shine abin da za mu tunkara."

@highlandre1, ya ce:

“Sanata, ka aika wa Baba guragurbin sunaye, don Allah a sakonka na gaba, ka saka Peter Obi da Sowore.
“Tsoffin 2 ba su da wani abin da za su baiwa al’ummar Najeriya, ko kuma za ka zabi ka nada wadannan biyun a matsayin shugabannin kamfanin ka a madadin Peter Obi da Kingsley Moghalu?

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

"Dole ne mu gyara!"

Burin Atiku a zaben 2023: Ina sa ran 'yan Najeriya za su yi kasa-kasa da jam'iyyar APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar adawa ta PDP, kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya koka da halin da kasar ke ciki, inda ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi waje da jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023 mai zuwa.

Da yake nuna rashin jin dadinsa game da gazawar tsarin mulkin APC, Atiku ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kai su tabbatar an kayar da APC a 2023 Vanguard ta ruwaito.

Ku tuna cewa dan takarar jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Sanata Bola Ahmed Tinubu, a makon da ya gabata ya aike da wani sakon murya kakkausar ga jam’iyyar PDP da ya ce kawai ta koma gefe ta shirya binne kanta a shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Zaben fidda gwanin APC: Taro ya yi dumi, Osinbajo ya fice daga Eagle Square

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.