Tsohon Hadimin Buhari Ya Ragargaji Peter Obi, Ya Bayyana Abin Da Yasa Tsohon Jigon Na PDP Ya Koma Labour Party

Tsohon Hadimin Buhari Ya Ragargaji Peter Obi, Ya Bayyana Abin Da Yasa Tsohon Jigon Na PDP Ya Koma Labour Party

  • Bashir Ahmad ya bugi kirji ya ce jam'iyyar Labour Party, LP, za ta roke shi ya zama mata dan takarar shugaban kasa a 2023
  • Tsohon hadimin shugaban kasar a bangaren sabon kafan watsa labarai ya furta hakan ne yayin da ya yi ikirarin cewa jam'iyyar ta LP bata yi fice a mafi yawancin jihohin arewa ba
  • A cewar Ahmad, dan takarar shugaban kasar LP, Peter Obi ya fice daga PDP ne don yana tsoron ba zai samu kuri'a ko daya ba a zaben fidda gwani

An yi yakin baka tsakanin Ahmad Bashir, tsohon hadimin Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren sabon kafar watsa labarai da jam'iyyar Labour Party, LP, da dan takarar shugaban kasarta, Peter Obi.

Amma, bisa alamu Ahmad ya fi sakin zafafan kalamai inda yayin kambama kansa ya yi ikirarin Obi ya fice daga jam'iyyar PDP ne don yana tsoron ba zai samu kuri'a ko daya ba a zaben fidda gwani na PDP.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Saka Labulle Da Lawan Da Ameachi a Aso Rock Villa

Tsohon Hadimin Buhari Ya Ragargaji Peter Obi, Ya Bayyana Abin Da Yasa Tsohon Jigon Na PDP Ya Koma Labour Party
Bashir Ahmed, Tsohon Hadimin Buhari Ya Ragargaji Peter Obi, Ya Bayyana Abin Da Yasa Tsohon Jigon Na PDP Ya Koma Labour Party. Hoto: (Photo: Ahmad Bashir, @PeterObi).
Asali: Facebook

Kafin hakan, tsohon hadimin na Shugaba Buhari ya bayyana cewa LP bata yi fice a Kano ba ya kuma yi ikirarin ba a damu da ita ba a mafi yawancin jihohin Najeriya har da Abuja.

Da ya ke kambama kansa, Ahmad ya yi ikirarin cewa ya tabbata LP za ta roke shi ya zama dan takarar shugaban kasarta, duba da karfinsa na fada a ji.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalamansa:

"Ka san cewa Labour Party ba ta da ofis a Kano, jihar da ke masu rajistan zabe fiye da 5,000,000, kuma bata da dan takara ko daya a kananan hukumomi 44 na jihar, haka batun ya ke a akalla jihohi 26 cikin 36 har da Abuja.
"Magoya bayan PO suna yawan tuna min kuri'un da na samu a zaben fidda gwani, suna manta cewa tsoron rashin samun kuri'a ko daya yasa jagoransu, Peter Obi ya tsere daga PDP ya koma karamar jam'iyyar LP, wacce na tabbata da matsayina, za a roke ni in karba tikitin takarar shugaban kasa."

Kara karanta wannan

2023: Hadimin Ganduje Ya Bayyana Dalilan da Suka sa Ya Dace Ya Zama Mataimakin Tinubu

El-Rufa'i: Buhari Ya Goyi Bayan Shawarar Da Muka Yanke Na Mayar Da Mulki Kudu a 2023

A wani rahoton, Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya dade yana goyon bayan matakin da gwamnonin arewa a APC suka dauka na mayar da mulki kudu a 2023.

Gwamnan na Jihar Kaduna ya bayyana hakan ne cikin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today a Channels Television.

Asali: Legit.ng

Online view pixel