Zaben Fidda Gwani: Yadda wasu 'Yan takaran APC suka kama gaibu, suka sha kashi a hannun Bola Tinubu
Wani sabon batu ya bayyana game da tabbacin da mukarraban Buhari suka baiwa 'yan takara a kalla shida a zaben fidda gwanin jam'iyyar APC da aka yi kwanan nan tare da bada tabbacin sune 'yan takarar da za su fafata a zaben 2023.
Duk irin kokarin da aka yi don ganin an tankade 'yan takarar 23 da suka siya fom din takarar shugaban kasar jam'iyya mai mulki ta APC a kan N100 miliyan bai yi wu ba yayin da suka dage a kan tsayawa takarar.
Bayan kokarin da shugabannin jam'iyyar a matakin kasa da yankuna da bai yi tasiri ba, gwamnonin 22 na jam'iyyar sun samo wata hanyar da za su yi tankade da rairaya don rage yawan 'yan takarar. Bayan ganawa da kwamitin ayyuka na kasa (NWC), sun zo da jerin sunayen 'yan takara biyar da za su fafata a filin zaben Eagle Square, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, bayan labarin ya yadu cewa gwamnoni sun mika sunayen Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi, ga shugaban kasa, sauran 'yan takara an yi watsi da su.
Daily Trust a ranar Lahadi ta ruwaito yadda kokarin da gwamnonin suka yi a baya bai yi tasiri ba. Hakan yasa 'yan takarar fafatawa a filin zaben.
An tattaro yadda 'yan takara da dama suka yi ta samun tabbaci daga mutane da dama cewa shugaban kasa zai mara musu baya duk da irin kayen da suka hango.
Dukkan 'yan takarar da suka dogara da shugaban kasa zai mara musu baya sun sha kaye. Tinubu, wanda shi ne mutum na farko da ya bayyanawa duniya ra'ayinsa na fitowa takarar shugaban kasa ne ya amshi tutar jam'iyyar da kuri'u 1,271.
Ahmad Ibrahim Lawan
Shugaban majalisar dattawa ne na karshen shiga gasar neman tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a APC.
Wasu awanni kafin zaben fidda gwanin, shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ya ambaci sunan Ahmad Lawan a matsayin 'dan takarar da jam'iyyar ta tsayar a ganawar da mambobin NWC suka yi. Sai dai, gwamnonin arewa da wasu masu rike da mukaman kudu sun kalubalanci hakan.
Daily Trust ta ruwaito yadda 'dan yayar shugaban kasa, Malam Mamman Daura, tsohon babban daraktan hukumar 'yan sandan farin kaya (DSS), Lawal Daura da Sanata Abdullahi Adamu suka mara wa Lawan baya.
Majiyoyi a Villa sun ce ukun sun yi nasarar shawo kan shugaban kasar, amma caccakar da shugaban jam'iyyar ya sha ne ya sa ya janye batun.
Bayan rushewar maganar sulhun da aka shirya, Lawan ya zo na hudu da kuri'u 152.
Rotimi Amaechi
Amaechi, tsohon ministan sufuri ya fara kamfen din zama shugaban kasa cike da dabara ta hanyan kwagiloli da ya yi a Daura, mahaifar shugaban kasa a jihar Katsina.
Manya a jerin kwangilolin sune jami'ar sufuri da titin jirgin kasan Kano zuwa Maradi da ya ratsa ta Daura, da dai sauransu.
Don shimfida ga kamfen dinsa, sarkin daura, Alhaji Umar Faruq ya nada Amaechi a matsayin Dan Amanar Daura.
Da taimakon 'dan yayar shugaban kasa kuma hadimin shugaban kasa na musamman, Sabiu Yusuf wanda aka fi sani da Tunde, Amaechi ya hadu da mutane da dama na hannun daman Buhari.
Baya ga Mamman Daura, Tunde ne wanda yafi kowa fadi a ji a fadar shugaban kasa, kamar yadda wadanda suka san abubuwan da ke wakana a Villa suka fadi.
Tare da taimakon fadi a jin da Tunde ke da shi, masu marawa Amaechi baya har zuwa rushewar sulhun da aka tsara, sun yi imani shi ne 'dan takarar da zai yi nasara.
Wasu manyan masu fadi aji sun bayyanawa Daily Trust cewa Amaechi ne 'dan takarar da shugaban kasa ke so.
'Yan Takarar Shugaban Kasa A APC Guda 7 Sun Ki Yarda Da Sunayen Mutum 5 Da Gwamnoni Suka Mika Wa Buhari
Tsohon gwamnan Ribas din ya tashi da kuri'u 316 a zaben fidda'dan takarar.
Yemi Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya yi kunnen uwar shegu da duk irin magiyar da aka masa a kan ya janyewa ubangidansa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
An samu rahoton yadda shugabannin kudu maso yamma na jam'iyyar suka rokesa ya janyewa Tinubu ana saura kwanaki biyu kafin zaben.
Sai dai ya dage a kan sai ya gwada sa'arsa.
Star-boy, kamar yadda magoya bayansa suke masa lakabi, ya zo na uku da kuri'u 235. Har zuwa kammala zaben fidda gwanin, magoya bayansa suna ganinsa a matsayin wanda zai zama zakaran gwajin dafi.
Sanata Godswill Akpabio
Gwamnan da ba kasafai ake samunsa ba', ya zama 'sanatan da ba kasafai ake samu ba', ministan kuma 'dan takarar shugaban kasar ya dogara da makusantan Aisha Buhari.
Sai dai, bayan gano mutanen da ke masa aiki ba za su iya yi masa abun da ya dace ba, ya janye wa Asiwaju.
Bayan marawa Asiwaju baya a zaben, Akpabio ya yanki tikitin tsayawa takarar sanatan Akwa Ibom na arewa maso yamma.
Ibikunle Amosun
Kamar Akpabio, Amosun, tsohon gwamnan jihar Ogun ya janyewa tsohon gwamnan Legas a zaben fidda gwanin. Yanke shawarar marawa Tinubu baya da ya yi ya ba mutane da dama mamaki, kamar yadda masu rike da mukaman APC na kudu maso yamma suka ce ba wani ga maciji suke ba.
Asali: Legit.ng