Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i

Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i

  • Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa yan Najeriya su daina shigar da addini harkar mulki, bal su damu da kwarewar mutum
  • El-Rufa'i ya yi martani kan masu cewa jam'iyyar APC kada su tsayar da Musulmi mataimakin Tinubu
  • Ba zamu taba yarda Tinubu ko Atiku su zabi Musulmi matsayin mataimakansu ba, kungiyar CAN

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya yi Alla-wadai da yadda mutane ke damun kansu kan maganar daukan Musulmi ya zama mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin hira a ChannelsTV ranar Juma'a.

Ya bayyana cewa mutumin kwarai ake bukata ya zama abokin tafiyar Tinubu kuma addininsa ba shi muhimmanci.

Yace:

"Bai kamata mu rika maganar addini ba. Idan na shiga jirgin sama, ba na tambayar sunan matukin jirgin. Idan na shiga asibiti, ba na tambayar addinin Likitan, kawai lafiya nike nema."

"Yadda yan jarida da wasu maras hankali ke kokarin cusa addini siyasa da mulki abin takaici ne kuma babu inda zai kai mu."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Ba addini zai magance mana matsala ba. Mutanen kirki kuma masu kwarewa ake bukata. A jihata na zabi mace kwararriya a zaben 2019, amma saboda Musulma ce an ce na zabi Musulmi kuma zan fadi, amma bamu fadi ba, mun yi galaba a zaben."

El-Rufa'i
Na zabi Musulma matsayin mataimakiyar gwamna kuma babu abinda ya faru, El-Rufa'i Hoto: Governor of Kaduna
Asali: UGC

Bamu yarda Musulmi da Musulmi su zama Shugaba da mataimaki ba: Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta gargadi jam'iyyun siyasa kada suyi kuskuren zaben Musulmi da Musulmi matsayin yan takaran Shugaban kasa da mataimaki a 2023.

Sakataren kasan na kungiyar, Joseph Bade Daramola, ya bayyana hakan ranar Juma'a a birnin tarayya Abuja, rahoton DailyTrust

A cewarsa, hakan na da hadari ga zaman lafiya da hadin kan yan Najeriya.

Ya yi kira ga Tinubu ya dauki mataimaki daga Arewa, Atiku ya dau Kirista daga kudu kuma Peter Obi ya dau Musulmi daga Arewa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel