‘Yan APC da suka yi nasara, da 'yan biyu-babu da wadanda su ka fi shan kunya a zaben gwani

‘Yan APC da suka yi nasara, da 'yan biyu-babu da wadanda su ka fi shan kunya a zaben gwani

  • Nasarar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a zaben fitar da gwani zai canza yadda siyasar APC ke tafiya
  • Akwai masu neman takarar da suka gyara alakarsu da Bola Tinubu a zaben tsaida ‘dan takaran
  • Wasu kuma sun sha kashi a zaben, ana tunani fito-na-fiton da suka yi ya nakasa su kenan a siyasa

Abuja - Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto a game da wadanda suka samu galaba da wadanda suka samu akasin haka a zaben fitar da gwanin APC.

Wadanda suka yi nasara

1. Bola Tinubu

Babban wanda ya yi nasara a zaben shi ne Bola Tinubu wanda ya samu tikiti da kuri’a 1271. Tinubu ya dade yana aiki domin ganin zuwan wannan ranar.

Kara karanta wannan

2023: A karon farko, Bola Tinubu ya tabo magana game da wanda zai zama Mataimakinsa

2. Gwamnonin Arewa

Wasu rukunin da zaben ya yi masu kyau su ne gwamnonin Arewa da suka dage a kan mikawa ‘dan kudu takara, kuma da-damansu suka samu yadda suke so.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

3. Kayode Fayemi

A dalilin janye takararsa da ya yi, Kayode Fayemi ya gyara alakarsa da Bola Tinubu. Ana yi masa zargin ya ci amanar tsohon Ubangidansa, yanzu ya wanke kansa.

4. Godswill Akpabio da sauransu

Ministan Neja-Delta shi ne ya fara bude kofar janye takararsa. Jaridar ta ce hakan zai taimakawa siyasar Godswill Akpabio da duk sauran wadanda suka bi sahunsa.

Bola Ahmed Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Wadanda suka yi asara

5. Abdullahi Adamu

Ana zargin shugaban APC na kasa da kokarin kakaba Ahmad Lawan a matsayin ‘dan takaran jam’iyya, amma hakarsa da ta Lawan ba ta cin ma ruwa a APC ba.

6. Ahmad Lawan

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya hakura da takarar ‘dan majalisa a zaben 2023, ya shiga neman tikitin takarar shugaban kasan da bai iya kai ko ina ba.

Kara karanta wannan

Barazana da kalubale 8 da Bola Tinubu ya fuskanta wajen zama ‘Dan takaran APC a 2023

7. Yahaya Bello

Rahoton ya ce Yahaya Bello ya ji kunya a zaben domin shi kadai ne gwamnan Arewa da bai goyon bayan mulki ya koma hannun kudu a 2023, ya kare ne da kuri'u 47.

8. Ben Ayade da David Umahi

Ana tunanin Gwamna Ben Ayade da Gwamna David Umahi sun dawo APC ne domin su samu takarar shugaban kasa a 2023, a karshe kuwa suka fadi war-was.

9. Rochas Okorocha

Sanata Rochas Okorocha ya fadi babu nauyi domin bai samu ko kuri’a daya a zaben ba. A zaben fitar da gwanin APC da aka yi na zaben 2015, ya tabuka abin kirki.

10. Rotimi Amaechi da sauransu

Ana sa Rotimi Amaechi a jerin ne ba domin ya sha kasa ba sai dai saboda ya ajiye kujerarsa ta Minista. Idan dai bai koma kujerarsa ba, ya yi biyu-babu kenan.

Ogbonnaya Onu da Emeka Nwajiuba su na cikin wadanda suka ajiye mukamansu a gwamnatin Muhammadu Buhari da nufin yin takara, amma suka sha kashi.

Kara karanta wannan

Burin 2023: Ajandoji 7 da Bola Tinubu ke da burin yiwa 'yan Najeriya idan ya gaji Buhari

11. Yemi Osinbajo

Babu wanda ya ji kunya a zaben tsaida gwanin irin Yemi Osinbajo domin na uku ya zo, sannan kuma ana yi masa kallon babban wanda ya ci amanar Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng