Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

  • Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje ya ce nasarar da Asiwaju Bola Tinubu ya samu a zaben fidda gwani na APC alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa
  • Ganduje, ta bakin sakataren watsa labarai, Abba Anwar ya taya jagoran na jam'iyyar APC murnar nasarar da ya samu bayan samun kuri'u 1,271
  • Gwamnan na Jihar Kano ya ce wannan nasarar na Tinubu za ta kara karfafa jam'iyyar ta APC har wadanda suka fice ma za su dawo a dinke kai wuri guda

Kano - Abdullahi Ganduje, gwamnan Jihar Kano, ya taya Asiwaju Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas, murnar samun nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa a jam'iyyar APC, rahoton The Cable.

Tinubu ya samu kuri'u 1,271 inda ya doke abokan fafatawarsa a zaben na fidda gwani da aka kammala a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

Kiristoci yan arewa 4 da dayansu zai iya zama abokin takarar Tinubu

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa
Zaben APC: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa, In JI Ganduje. Hoto: @thecableng.
Asali: Facebook

A cikin wata sanarwa da Abba Anwar, babban sakataren watsa labarai, Ganduje ya ce nasarar da Tinubu ya samu a zaben fidda gwanin alama ce da ke nuna ya samu karbuwa a arewa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Nasarar Tinubu za ta karfafa jam'iyyar APC, Ganduje

Gwamnan na Kano kuma ya ce nasarar ta Tinubu za ta karfafa jam'iyyar kuma wadanda suka fice daga jam'iyyar ma su dawo.

"Gagarumin nasarar Asiwaju Bola Tinubu a zaben fidda gwani da aka kammala na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya nuna karbuwa sosai da ya samu a arewa, a matsayinsa na mai hada kan al'umma," in ji sanarwar.
"Wannan matakin na kishin kasa zai hada kan sassan kasar daban-daban.
"Aikin Shugaban kasa shine tabbatar da cewa an bi tsarin demokradiyya yayin gudanar da zaben kuma hakan abin yaba wa ne kuma abin koyi."

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Malik Ado-Ibrahim ya lashe tikitin takarar a YPP ta su Adamu Garba

Ganduje: Nasarar Tinubu a APC Alama Ce Da Ke Nuna Ya Samu Karbuwa a Arewa

INEC: Yan Najeriya Na Son Ma'aikatan Mu Su Bi Su Har Gida Su Kai Musu Katin Zabe

A wani rahoto, cikin sabbin masu zabe 34,000 da suka yi rajista daga watan Yuni zuwa Disamba a Legas, 3,000 kawai suka karbi katin zabensu na dindindin (PVC) a cewar kwamishinan zabe na Legas, Olusegun Agbaje.

Agbaje ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai wurin wani taron wakoki da aka yi don wayar da kan matasa kan zabe a Tafawa Balewa Square Legas, yana mai nuna rashin dadinsa kan rashin karban katin, rahoton Daily Trust.

Ya kara da cewa hukumar ta umurci jami'anta a kananan hukumomi su kira masu zabe su fada musu su taho su karbi katinsu amma ba su samun amsa gamsassu, wasu masu zaben ma cewa suke yi a kawo musu PVC din gidansu.

Kara karanta wannan

Yanzu: Atiku Da Gwamnonin PDP Sun Shiga Taron Sirri Bayan Nasarar Tinubu A Zaben Fidda Gwanin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel