Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023

  • Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan shugabancin Bola Tinubu ba
  • Lamido ya yi hasashen cewa Buhari na kokarin ganin ya tsayar da Rotimi Amaechi da Ahmed Lawan domin su gaje shi a 2023
  • Sai dai kuma, dan siyasar ya bayyana cewa Tinubu ne kadai zai iya karawa da jam'iyyarsa ta PDP har ma ya bata ciwon kai a cikin dukkanin masu neman tikitin APC

Babban jagoran jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Sule Lamido, ya ce yana hasashen juyin mulki a zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Lamido ya ce wannan juyin mulki ne zai kai ga samar da tikitin shugaban kasa na shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da tsohon ministan sufuri Rotimi Amaechi.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, yayin da yake zantawa da jaridar Vanguard.

Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya yarda cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne kadai dan takarar shugaban kasa na APC da zai iya ba jam’iyyarsa ta PDP ciwon kai.

Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023
Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba: Sule Lamido ya bayyana mutum 2 da Buhari yake so ya tsayar a 2023 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sai dai kuma, ya ce Tinubu ba zai taba zama dan takarar jam’iyyar mai mulki ba a zaben shugaban kasa da za a yi a watan Fabrairun 2023.

A makon da ya gabata ne tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na PDP.

Lamido ya kuma bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ya zama shugaban kasa ba saboda tunaninsa.

Jaridar Vanguard ta nakalto Lamido yana fadin:

“A yanzu haka, Tinubu na tsaka mai wuya daga wa? Yan uwansa a kungiyar Afenifere wadanda suka fito karara suka nuna basa son shi da kuma gwamnonin APC da suka suna basa son shi saboda sun ce yana da izza da iko. Ina nufin, shi dansu ne, me zai sa ba za su iya sanya shi ba?

Kara karanta wannan

Hotuna: 'Yan a mutun Jonathan sun mamaye hedkwatar APC suna neman a ba shi tikiti

“Ku lura da maganganuna, Buhari ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na san tunanin mutumin. Ba zai taba goyon bayan Tinubu ba. Na fada amma mutane basu yarda dani ba amma ku zuba ido ku gani. Abun gaba daya ba game da Tinubu bane ko ra’ayin wasu. Ba ma don Najeriya bane sai don wasu muradai na gashin kai. Babu yadda za a yi Buhari ya marawa Tinubu baya, saboda gaba daya abun zai karkata ga ra’ayin kai.
“Mu yi magana ta gaskiya, a yau Tinubu yana rawarsa ne shi kadai. Dubi abun da ya yi amma a yanzu suna ce masa a’a.
“Idan kudu ta shirya lashe zabe, dan takara daya da zai iya fafatawa da PDP don kudinsu shine Tinubu. Yana da nufi mai kyau. Yana da iyali na siyasa. A Najeriya a yau, koda APC bata bashi tikiti ba, zai lashe zabe saboda Najeriya na son komai baya ga Buhari.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: APC ta magantu kan batun takarar Jonathan a zaben fidda gwanin shugaban kasa

“Na fadi Buhari ba zai ba Tinubu ba, yana kokarin hada Amaechi da Lawan.
“Ina hangen juyin mulki.”

2023: El-Rufai, Zulum da sauran gwamnonin arewa masu goyon bayan kudu maciya amana ne – Kungiyar arewa

A wani labarin, wata kungiya mai kare muradin arewa ‘Northern Interests Coalition’ ta soki gwamnonin arewa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) su 10 wadanda suka goyi bayan mika mulki yankin kudu a 2023, jaridar Punch ta rahoto.

Kungiyar gwamnonin APC daga arewa ta goyi bayan kudu ta samar da shugaban kasar Najeriya na gaba a taron na ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng