Bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani, dan’uwan Buhari ya yi barazanar tarwatsa APC

Bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani, dan’uwan Buhari ya yi barazanar tarwatsa APC

  • Dan majalisa mai wakiltan mazabar Sandamu/Daura/Maiadua a majalisar wakilai, Fatuhu Muhammad ya sha alwashin dawo da tikitinsa bayan shan kaye a zaben fidda gwani
  • Fatuhu wanda ya kasance dan'uwan shugaban kasa Buhari ya kuma sha alwashin tarwatsa jam'iyyar mai mulki a jihar Katsina idan har ba a dawo masa da tikitinsa ba
  • Ya ce zai koma jam'iyya mai kayan marmari ta NNPP sannan ya ga wa talakawa za su zaba a tsakanin shi da APC

Katsina - Dan majalisa mai wakiltan mazabar Sandamu/Daura/Maiadua ta tarayya a Katsina, Fatuhu Muhammad, ya yi barazanar lalata jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar.

Ya kuma sha alwashin komawa jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin zanga-zanga kan rashin adalcin da aka yi masa a yayin zaben fidda gwamnin jam’iyyar da aka kammala.

Kara karanta wannan

Rikici: Zai zama bala'i idan APC ta hana Tinubu tikitin takarar shugaban kasa, Shettima

Mista Muhammad, dan’uwan shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha kaye a hannun Aminu Jamo wanda ya samu kuri’u 117 yayin da shi kuma ya samu kuri’u 30.

Bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani, dan’uwan Buhari ya yi barazanar tarwatsa APC
Bayan ya sha kaye a zaben fidda gwani, dan’uwan Buhari ya yi barazanar tarwatsa APC Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Premium Times ta rahoto cewa a wata hirar wayar tarho wanda tuni ya shahara, Mista Muhammad ya yi barazanar dawo da tikitinsa da aka sace ko kuma ya bar jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A faifan muryar mai tsawon minti shida da sakwan 22 da jaridar ta samu, an jiyo dan majalisar yana fadama wani da yake da kira a matsayin Ranka ya dade, cewa zai lalata APC a jihar Katsina.

Ya ce ba zai shiga sabon zabe ba idan jam’iyyar ta yanke shawarar yin haka domin shine ainahin wanda ya lashe zaben fidda gwanin da aka yi a makon da ya gabata.

Ya ce:

“Ba za su iya yin kowani zabe ba saboda ni na lashe wannan yayin da suka karya doka. Kamata ya yi ake kawai sun mayar mun da tikiti na, ko kuma mu hadu a kotu ko na lalata jam’iyyar sannan na kawo sabuwar jam’iyya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ina zama shugaban kasa zan saki shugaban IPOB Nnamdi Kanu, dan takara

“Zan ma iya zuwa na kawo jam’iyyar kayan marmari (NNPP) sannan kawai za su ga jam’iyyar Kwankwaso a Daura. Eh, ina aikata haka saboda kowa kansa yake yiwa yaki. Su zo su fadama talakawa abun da suka yi masu. Nima zan fadi abun da na yi ma talakawa sannan mu ga wa talakawa za su zaba.”

Mista Muhammad ya ce ba a iya garin shugaban kasar Daura kadai zai lalata jam’iyyar ba, harma ga jihar gaba daya.

Ya ce:

“Na rantse, zan lalata APC a jihar Katsina saboda kamar yadda yake a yanzu, a Funtua da sauran wurare, Nura Khalid dan takarar gwamna na NNPP da mutanensa suna jirana amma na nemi su dan tsaya kadan. Toh wani dalili ne zai sa na bari wani ya dunga wahalar da ni a mahaifata? Idan tsarin sarauta ne, wa zai karbi mulki daga shugaban kasa idan ba ni ba saboda na fito daga bangaren uba ne.

Kara karanta wannan

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

“Wasu daga cikinsu da basu da alaka da shi (shugaba Buhari) ba za su zo sannan su dunga ikirarin sune ainahin mutanen Buhari ba saboda kawai muna dauke idanu daga kiransu a yadda suke.”

Yayin da yake ba dayan wanda suke waya da shi tabbacin cewa ba zai yi amfani da rikici wajen dawo da tikitinsa ba, ya ce shi ba yaron kowa bane a fagen siyasa don haka ba zai watsar da tikitinsa ba.

Sai dai kuma, bai yi bayanin yadda aka wadanda yake kira da makiyansa suka kwace masa tikitin ba.

2023: Atiku ya nemi hadin kan Wike, Saraki da sauran jiga-jigan PDP don lallasa APC

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya nemi goyon bayan abokan hamayyarsa a jam’iyyar domin kayar da APC mai mulki a babban zabe mai zuwa.

Atiku ya bayyana hakan ne a ranar Laraba bayan ya amshi shaidar zama dan takara na jam’iyyar a sakatariyar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja.

Kara karanta wannan

Allah ne ya kama ka: Mawaki Davido ya zolayi hadimin Buhari da ya sha kaye a zaben fidda gwani

A cewar tsohon mataimakin Shugaban kasar wanda ya shafe kimanin shekaru 30 yana son zama shugaban kasar Najeriya, babbar abokiyar hamayyarsa ita ce APC amma ba wai abokan takararsa na zaben fidda gwanin PDP da aka yi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng