Allah ne ya kama ka: Mawaki Davido ya zolayi hadimin Buhari da ya sha kaye a zaben fidda gwani

Allah ne ya kama ka: Mawaki Davido ya zolayi hadimin Buhari da ya sha kaye a zaben fidda gwani

  • Shahararren mawaki Davido ya yi ba a ga tsohon hadimin shugaban kasa, Bashir Ahmad, kan kaye da ya sha a zaben fidda gwanin APC
  • Davido ya nuna cewa Allah ne ya kama Ahmad sakamakon kulla-kulla da suka yi a lokacin zaben jihar Osun
  • Tsohon hadimin shugaban kasar dai ya gaza samun tikitin takara na dan majalisa mai wakiltan mazabar Gaya/Ajingi/Albasu/ a majalisar tarayya

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Fitaccen mawakin Najeriya, Davido, ya zolayi tsohon hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, wanda ya sha kaye a zaben fidda gwanin jam’iyyar APC.

Mista Ahmad, wanda ya nemi takarar tikitin dan majalisa mai wakiltan mazabar Gaya/Ajingi/Albasu/ a majalisar tarayya, ya samu kuri’u 16 kacal inda ya sha kaye a hannun Abdullahi Gaya wanda ya samu kuri’u 109 a zaben fidda gwanin.

Allah ne ya kama ka: Mawaki Davido ya zolayi hadimin Buhari da ya sha kaye a zaben fidda gwani
Allah ne ya kama ka: Mawaki Davido ya zolayi hadimin Buhari da ya sha kaye a zaben fidda gwani Hoto: theguardian.com/Twitter/ @BashirAhmaad
Asali: UGC

Da yake martani ga kayen da Ahmad ya sha, mawakin ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa Allah ne ya kama tsohon hadimin shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Ya kwatanta lamarin da abun da ya faru a zaben jihar Osun, yana mai cewa duk abun da mutum ya shuka ita yake girba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya batun zaben Osun.....Duk abun da mutum ya shuka shi yake girba"

Bashir Ahmed Ya Yi Watsi Da Sakamakon Zaɓe a Kano

Tuni dai Ahmad ya yi watsi da sakamakon zaben fidda gwanin sannan ya nemi a sake gudanar da sabon zabe.

A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar 28 ga watan Mayu, Bashir ba zai amince da sakamakon zaben ba domin abubuwan da suka faru a wurin zaben sun janyo cikas na inganci da nagartan zaben, kuma idan ya yi shiru bai yi wa mutanensa da jam'iyyar APC adalci ba.

A cewarsa, an hana mafi yawa cikin daliget dinsa shiga wurin zaben ballantana su kada kuri'arsu, sannan babu wata takardan zabe dauke da sa hannun wakilansa don ba a bari ma sun shiga wurin zaben ba.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

Asali: Legit.ng

Online view pixel