Gwamnonin Arewa 9 su na goyon APC ta tsaida ‘dan Kudu ya zama Shugaban kasa a 2023

Gwamnonin Arewa 9 su na goyon APC ta tsaida ‘dan Kudu ya zama Shugaban kasa a 2023

  • Gwamnoni su na ta zama a kan wanda ya kamata ya zama ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Wasu Gwamnonin Arewa sun hakikance a kan cewa a 2023, ya kamata mulki ya bar yankin na su
  • A gefe guda kuma wasu su na da ra’ayin ‘dan kudu ba zai iya doke Atiku Abubakar da PDP a zabe ba

Abuja - Akalla gwamnoni tara daga Arewacin Najeriya su na kira ga abokan aikinsu a jam’iyyar APC da aka dauko ‘dan takarar shugaban kasa yankin kudu.

Premium Times ta fitar da rahoto a yammacin Alhamis, 2 ga watan Yuni 2022 da ya nuna cewa wasu gwamnonin Arewa sun sallama a ba ‘dan kudu takara.

An dade ana tunanin jam’iyyar APC za ta fito da ‘dan takarar shugaban kasa a zaben 2023 daga kudancin Najeriya, kafin Atiku Abubakar ya samu tikitin PDP.

Kara karanta wannan

Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

Tun da jam’iyyar PDP ta ba ‘dan Arewa takara, sai lissafin APC mai mulki yake neman ya canza.

Rahoton ya ce gwamnonin APC sun yi ta yin zama domin fito da wanda zai yi wa jam’iyya takarar kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa, amma kai ya ki haduwa.

Kudu v Arewa

A halin yanzu APC ta na da gwamnoni 14 daga bangaren Arewa da takwas daga kudancin Najeriya. Wannan ya jawo aka gagara cin ma matsaya har yau.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin Arewa
Taron Gwamnonin Arewa Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Kan gwamnonin da suka fito daga jihohin Arewa (yankin da ke rike da mulki) ya rabu, su kuwa gwamnonin kudu sun hadu a kan su ne suka dace da takara.

Yadda gwamnoni suka rabu

Gwamnonin da suke ganin ya kamata Arewa ta hakura da neman mulki sun hada da: Farfesa Babagana Zulum, Simon Lalong, sai Abdullahi Umar Ganduje.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC su na tunanin mikawa Buhari sunayen mutum 2, sai ya zabi Magajinsa

Haka zalika a sahun wadannan gwamnoni akwai AbdulRahman AbdulRazaq, Abubakar Sani Bello, Aminu Bello Masari, Abdullahi Sule, da Nasir El-Rufai.

Jaridar ta ce gwamnonin Kaduna, Borno da Filato sun fi dagewa a kan wannan magana yayin da gwamnonin Kwara, Kano da Katsina ba su dauki abin da zafi ba.

Nan fa daya!

Amma duk da haka wadannan gwamnoni sun samu sabani a kan wanda ya dace a tsaida ko da an yarda mutumin kudu ne zai karbi shugabanci a Mayun 2023.

Gwamna Ganduje yana son Tinubu, shi kuwa Lalong burinsa Rotimi Amaechi ya karbi mulki, Gwamnonin Neja da Nasarawa su na son Tinubu ne da Osinbajo.

Ra'ayin mutanen Tinubu

Dazu aka ji labari cewa wasu daga cikin magoya bayan Asiwaju Bola Tinubu sun ce ana kokarin zagaye gwaninsu a APC ta hanyar watsi da zaben fitar da gwani.

Tinubu Support Organisation da Northern Young Professionals for Tinubu sun fito, sun yi magana, sun ce ba za su yarda da maganar fito da 'dan takara ta maslaha ba.

Kara karanta wannan

2023: Buhari ya lissafa sharuddan da dole 'dan takarar shugabancin kasa na APC ya cika

Asali: Legit.ng

Online view pixel