Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

Rudani: Sabbin bayanai sun fito, yayin da gwamnonin APC ke shawari kan zaban magajin Buhari

  • Gabanin zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, gwamnonin da aka zaba a dandalin jam’iyyar a yanzu suna neman wanda za su zaba a matsayin wanda zai gaji Buhari
  • Shugaba Buhari ya yi wani taro a ranar Talata, 31 ga watan Mayu da gwamnoni, ya bukaci gwamnonin da su taimaka masa a wannan gagarumin aiki
  • Sai dai taron da gwamnonin suka yi dangane da ci gaban bai haifar da wani sakamako ba, kuma sun amince za su sake haduwa a cikin wannan mako

Abuja - Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki sun fara neman hanyar tsayar da dan takarar shugaban kasa na bai daya bayan umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Wata majiya mai tushe a taron farko na gwamnonin ta bayyana cewa taron ya kare ne ba tare da tsayar da matsaya daya ba, inji rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Wasu Makusanta da Mukarraban Shugaban kasa 7 da suka gagara samun takara a APC

Majiyar ta shaida cewa:

“Babu wata yarjejeniya tukuna. An dage taron zuwa karshen makon nan.”

Zabar dan takarar APC: Me ya faru a taron gwamnonin?

Da aka tambayi majiyar da ba a bayyana sunan ta ba a kan abin da ya faru a taron, ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Har yanzu gwamnonin suna rabe kan lamarin. Ana la'akari da abubuwa da yawa, ciki har da iyawa, yanki da addini."

Ku tuna cewa shugaban kasa a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, ya bukaci gwamnonin APC da su nemo wanda zai gaje shi daidai lokacin da ake ci gaba da tantance 'yan takarar APC.

Jigon APC: Kada ku mai da zaben fidda gwanin shugaban kasa dandalin ruwan daloli

A wnai labarin, Daily Sun ta rahoto cewa, jigon jam’iyyar APC, Mista Gbenga Olawepo-Hashim, ya yi gargadin cewa kada zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ya zama wani taron ruwan daloli da kuma dandalin ciniki.

Kara karanta wannan

Kaduna: An Sako Ƴar Dr Ramatu Bayan Shafe Kwana 38 a Hannun Ƴan Bindiga

A wata sanarwa da ta fito daga ofishinsa da ke Abuja, a ranar Talata, ya bayyana cewa, kasar nan ba wata kaya ce da za a yi cinikinta ba, kuma ba wata kadara ce da za a yi gwanjonta ba da sayar da ita ga mai kudi.

Ya kuma kara da cewa, ba a taba sayar da shugabancin kasa ba ba za a fara ba yanzu, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel