Zaben fidda gwanin APC na dan takarar majalisar tarayya a Yobe ya bar baya da kura

Zaben fidda gwanin APC na dan takarar majalisar tarayya a Yobe ya bar baya da kura

  • Jayayya ya barke kan sakamakon zaben dan takarar da zai wakilci mazabar Bade/Jakusko na jam'iyyar APC a jihar Yobe
  • Dan majalisa mai ci, Zakariya Yua Galadima, ya yi ikirarin cewa shine ya lashe zaben, inda ya yada sakamakon zaben
  • Sai dai kuma wasu yan takara da deleget din jam'iyyar sun ce sam ba a yi zaben ba kamar yadda aka tsara, hasali ma sun ce babu jami'in INEC ko na jam'iyyar da ya je wajen

Kwanaki shida bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar da zaben fidda gwaninta a fadin kasar domin zabar yan takararta na majalisun dokokin tarayya, wani rikici ya kunno kai a zaben wanda zai wakilci mazabar Bade/Jakusko a jihar Yola.

Yayin da dan majalisa mai ci, Zakariya Yua Galadima, ya yi ikirarin cewa shine ya lashe zaben, sauran yan takara sun ce ba a gudanar da zabe ba.

Kara karanta wannan

Jerin sunayen 'yan takara 5 da ake sa ran Buhari zai zabi daya don ya gaje shi

Wasu deleget sun yi zargin cewa sun shafe tsawon ranar a masaukin gwamnati na Gashua, wajen zaben fidda gwanin, amma daga jami’an INEC har na jam’iyyar babu wanda ya zo wajen, Premium Times ta rahoto.

Zaben fidda gwanin APC na dan takarar majalisar tarayya a Yobe ya bar baya da kura
Zaben fidda gwanin APC na dan takarar majalisar tarayya a Yobe ya bar baya da kura Hoto: The Punch
Asali: UGC

Mambobin jam’iyyar wadanda suka zanta da jaridar Premium Times, sun dasa ayar tambaya kan dalilin da yasa zabe ya gudana a sauran mazabu na jihar amma aka yi biris da na Bade/Jakusko.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun roki shugabancin jam’iyyar a jihar da na kasa da su shigo lamarin domin guje ma karya doka da oda.

Daya daga cikinsu, Mohammed Saleh, ya ce an gudanar da zaben fidda dan takarar sanata na wannan yankin a ranar Asabar a wajen da aka shirya yin zaben, amma jam’iyyar ta yi shiru game da zaben na majalisar wakilai.

Sai dai kuma, wani takardar sakamakon zabe na mazabar, da ke nuna Mista Galadima a matsayin wanda ya lashe wannan zaben da aka ce ba a yi ba, yana nan yana yawo.

Kara karanta wannan

Mataimakin Atiku Abubakar a zaben 2023 zai iya zama Gwamnan da ya yi takara da shi

Amma dan majalisar ya yi ikirarin cewa sakamakon zaben da ke yawo sahihi ne.

Mista Galadima ya ce:

“A iya sanina, nine na lashe zaben. Bana kera sakamako. Don haka abun da kuka gani shine sakamakon da ya ayyana ni a matsayin wanda ya yi nasara.”

Wani dan takara, Sani Ahmed Kaitafi, ya ce an tsara sakamakon ne.

Ya fadama magoya bayansa cewa ba a gudanar da zaben ba. Ya ce ya saba damokradiyya a hana deleget yin aikinsu na zabar wakilin jam’iyyar.

Hakazalika, magoya bayan wani dan takara, Mohammed Manu Girgir, sun ce ba a yi kowani zabe a mazabar ba.

Kokarin jin ta bakin shugaban jam’iyyar, Muhammad Gadaka, da sakataren jam’iyyar, Abubakar Bakabe, ya ci tura.

Da aka tuntube shi don jin ta bakinsa, sakataren INEC a jihar Yobe, Abubakar Abatcha Dikwa, ya ce ba zai iya tabbatar da ingancin sakamakon da ke yawo ba har sai ya samu rahoto daga jami’an zabe na kananan hukumomin biyu da ke mazabar.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

2023: Fitaccen dan siyasar arewa ya lissafa yan takarar APC 4 da za su iya tikar da Atiku a kasa

A wani labarin, Farouk Aliyu, tsohon shugaban marasa rinjaye a majalisar wakilai, ya ce jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki na da yan takara biyar da za su iya lallasa dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, a 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku ne ya mallaki tikitin PDP na babban zaben 2023 mai zuwa bayan ya kasar da babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

A wata hira da Channels TV, Aliyu ya lissafa yan takara hudu cikin biyar da yake ganin za su iya kayar da Atiku idan suka lashe tikitin jam’iyyar mai mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel