Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023

Gabannin babban zaben 2023, yan siyasa a fadin kasar na ta fafutukar neman mukamai daban-daban tare da kokarin ganin sun samu fifiko kan abokan hamayyarsu musamman a zaben fidda yan takarar jam'iyyu wanda shine farko.

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Wani binciken jaridar The Nation ya nuna cewa kusan rabin yan majalisar dattawa ta tara mai mambobi 109 ba za su samu damar komawa zauren ba a shekara mai zuwa.

Adadin na iya karuwa yayin da sakamakon zaben fidda yan takara na majalisar dattawa da jam’iyyun Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC) suka yi ke ci gaba da fitowa.

Wadannan jam’iyyu biyu sune ke da mafi rinjaye na yan majalisar a yanzu haka.

Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023
Jerin sunayen sanatoci 42 da ba lallai su koma majalisar dattawa ba a 2023 Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Baya ga wadanda suka rasa kudirinsu na komawa majalisar a zaben fidda gwani, sauran wadanda ba za su samu komawa ba harda masu neman tikitin shugabancin kasa a jam’iyyunsu da wadanda suka yi nasara ko suka gaza samun tikitin gwamna.

Kara karanta wannan

APC: Dan majalisan Arewa da ake zargi da badakalar kudin Korona ya rasa tikitin tazarce

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Manyan jiga-jigan majalisar uku da ke neman shugabancin kasa

  1. Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan
  2. Mataimakin mai tsawatarwa a majalisa, Ajayi Boroffice
  3. Sanata Ibikunle Amosun

Sanatocin da suka lashe tikitin gwamna sune

  1. Mataimakin shugaban majalisar dattawa , Ovie Omo-Agege - APC, Delta ta tsakiya
  2. Uba Sani - APC, Kaduna ta tsakiya
  3. Teslim Folarin - APC, Oyo ta tsakiya
  4. Sanata Sandy Onor - PDP, jihar Cross River
  5. Aishatu Dahiru Ahmed – APC, Adamawa ta tsakiya
  6. Emmanuel Bwacha - APC, Taraba ta kudu

Wadanda suka fadi a tseren gwamna a jihohinsu

  1. Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe - PDP, jihar Abia
  2. George Sekibo - PDP, Rivers ta gabas
  3. Gershom Bassey - PDP, Cross River ta kudu
  4. Shugaban majalisar dattawa Yahaya Abdullahi – APC, Kebbi ta arewa
  5. Yusuf Yusuf - APC, Taraba ta tsakiya
  6. James Manager - PDP, Delta ta kudu
  7. Sanata Ike Ekweremadu - Enugu ta yamma

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Abaribe wanda ya janye daga tseren a ranar Talata da ya gabata, ya sauya sheka daga PDP zuwa All Progressive Grand Alliance (APGA) don sake tseren sanata.

Wadanda suka sha kaye a hannun abokan hamayyarsu

  1. Sanata Ibrahim Yahaya Oloriegbe - APC, Kwara ta arewa
  2. Tolu Odebiyi - APC, Ogun ta yamma
  3. Aliyu Sabi Abdullahi - APC, Niger ta arewa
  4. Bulus Amos - APC, Gombe ta kudu
  5. Bello Mandiya - APC, Katsina ta kudu
  6. Barkiya Abdullahi - APC, Katsina ta tsakiya
  7. Olubunmi Adetunmbi - APC, Ekiti ta arewa
  8. Frank Ibezim - APC, Imo ta arewa
  9. Danjuma La’ah - PDP, Kaduna ta kudu
  10. Cleopas Zuwoghe - PDP, Bayelsa ta tsakiya
  11. Matthew Urhoghide - PDP, Edo ta kudu
  12. Ayo Akinyelure - PDP, Ondo ta tsakiya
  13. Nicholas Tofowomo - PDP, Ondo ta kudu
  14. Smart Adeyemi - APC, Kogi ta yamma
  15. Ezenwa Francis Onyeawuchi - PDP, Imo ta gabas
  16. Danlandi Sankara - APC, Jigawa ta arewa maso yamma

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

Wadanda suka janye daga tseren

  1. Francis Alimikhena - APC, Edo ta arewa
  2. Godiya Akwashiki - APC, Nasarawa ta kudu
  3. Adamu Aliero - APC, Kebbi ta tsakiya

Wadanda basa neman tazarce

  1. Sanata Oluremi Tinubu - APC, Lagos ta tsakiya
  2. Chukwuka Utazi - PDP, Enugu ta arewa
  3. Emmanuel Orker-Jev - PDP, Benue ta arewa maso yamma
  4. Oseni Yakubu - APC, Kogi ta tsakiya
  5. Theodore Orji - PDP, Abia ta tsakiya
  6. Sanata Adamu Abdullahi - Ya yi murabus don zama shugaban APC na kasa
  7. Abubakar Kyari - Ya yi murabus don zama mataimakin shugaban APC na kasa (arewa)

Tashin hankali: Cikin 'yan tawagar Tinubu ya duri ruwa, yayin da ake ci gaba da tantance 'yan takara

A wani labarin, mun ji cewa ana zaman zullumi a sansanin siyasar dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, yayin da Cif John Odigie-Oyegun ke jagorantar kwamitin tantance masu neman takara.

Kara karanta wannan

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

Ana ganin akwai takun saka tsakanin Odigie-Oyegun, tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa da babban jagoran jam’iyyar na kasa tun a lokacin zaben gwamnan jihar Edo na 2020.

Oyegun ne ke jagorantar kwamitin mutum bakwai don tantance masu neman takarar shugaban kasa na APC a yau Litinin a Abuja gabannin taron jam’iyyar, jaridar Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng