2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen Shugaban Kasa, Tinubu Ya Taya Atiku Murna

  • Jagoran jam'iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar murnar lashe tikitin takarar zaben shugaban kasa na PDP a 2023.
  • Amma ya tunatar da Atiku cewa akwai babban kalubale a gabansa na yi wa yan Najeriya bayanin dalilin da yasa jam'iyyarsa ta PDP ta shafe shekaru 16 kan mulki ba tare da tsinana wani abin a zo a gani ba.
  • Tsohon gwamnan na Jihar Legas ya kuma shawarci sauran masu ruwa da tsaki a siyasar su saka kishin kasa da cigaban yan Najeriya ya zama a gaba yayin babban zaben na 2023 a maimakon bita da kulli ko gaba

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jagoran jam'iyyar APC na ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar nasarar lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP na zaben 2023, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Atiku ya dauki wasu manyan alkawara, ya caccaki APC

Atiku ne ya samu ƙuri'u mafi rinjaye a zaben fidda gwanin da aka yi a Moshood Abiola Stadium Abuja ranar Asabar.

Tinubu ya jinjina wa Atiku bisa kishin kasarsa da jajircewa wurin ganin cigaban Najeriya.

2023: Da Yardar Allah Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen 2023, Tinubu Ya Taya Atiku Murna
2023: Insha Allahu Ni Da Kai Zamu Fafata a Zaɓen 2023, Tinubu Ya Taya Atiku Murna. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya kuma yaba wa sauran yan takarar saboda yadda suka yi zaben cikin natsuwa da kuma yin alkawarin mara wa Atikun baya.

Ya ce yana fatan tsohon mataimakin shugaban kasar, wanda kuma shine ɗan takarar jam'iyyar na PDP a zaben 2019, ya zama wanda za su fafata a zaɓen shugaban kasa na 2023 da izinin Allah da kuma taimakon daliget na APC.

The Punch ta rahoto cewa jagoran na APC ya ce nasarar Atiku bai bashi mamaki ba saboda kwarewarsa a matsayin dattijon ƙasa kuma wanda ya daɗe yana takarar shugaban kasa tun 1993.

Kara karanta wannan

Na yi farin ciki da kasancewa dan takarar PDP a zaben 2023 – Atiku Abubakar

Mu ajiye gaba da kiyayya mu fuskanci batutuwan da za su kawo cigaban kasa - Tinubu

Tinubu ya kara da cewa zaben da ke tafe kamata ya yi ya zama kan batutuwa da za su kawo cigaban Najeriya; samar da zaman lafiya, cigaba, magance matsaloli na zamantakewa da tsaro da ke addabar kasar a halin yanzu.

"Ina maraba da nasarar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaben da aka kammala na fidda gwani. Ina fatan fafatawa da shi a babban zaben da ke tafe. Na san tsohon mataimakin shugaban kasar a matsayin gwarzon ɗan siyasa mai kishin kasa kuma ya yi imani da hadin kai da cigaban kasar mu.
"A yayin da muke fuskantar zabe, ina kira ga ɗan takarar na PDP da sauran yan siyasa a dukkan jam'iyyu mu zama cewa mun yi siyasa ba da gaba ba.
"Mu mayar da hankali wurin yin kamfen kan abubuwa da za su inganta rayuwar yan Najeriya da samar da zaman lafiya ba cikin aminci da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

"Sai dai, dan takarar na PDP zai fuskanci kallubalen yi wa yan Najeriya bayani kan dalilin da za su zabe shi duba da cewa sun shafe shekaru 16 kan mulki ba tare da tabuka wani abin azo a gani ba.
"Har yanzu yan Najeriya ba su manta da rusa kasa da tattalin arziki da PDP ta yi ba cikin shekaru 16 da ta yi mulki kuma wannan abin zai shafi dan takarar na PDP yayin kamfen dinsa.
"Duk da haka, ina sake taya tsohon mataimakin shugaban kasar mu murnar yin nasara a zaben fidda gwani na jam'iyyarsa."

2023: Gudaji Kazaure Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin APC a Jigawa, Akwai Yiwuwar Zai Koma NNPP

A wani rahoton, Muhammad Kazaure, fitaccen dan majalisar nan mai wakiltar mazabar Kazaure/Roni/Gwiwa da Yankwashi a Jihar Jigawa na majalisar tarayya bai samu tikitin tsayawa takara ba a jam’iyyar APC, Premium Times ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Halin da Atiku, Saraki, Tambuwal, da Wike suke ciki a wajen zaben zama ‘dan takaran PDP

Kazaure ya na da jikakkiya da Gwamna Muhammad Badaru na jihar, tare da kuma jam’iyyar, reshen jihar Mukhtar Zanna, shugaban karamar hukumar Kazaure ne ya kayar da shi.

Zanna ya samu kuri’u 89, na kusa da shi kuma Muhammad Zakari mai kuri’u 70 yayin da Kazaure ya samu kuri’u 26.

Muhammad Alhassan, wanda soja ne mai murabus, sannan ya rike mukamin Kwamishinan Noma a jihar, ya samu kuri’u 8, sai Abdullahi Mainasara mai kuri’u 7.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

iiq_pixel