Zaben fidda gwanin PDP: Ba zan daga wa kowa kafa ba, Gwamna Bala Mohammed

Zaben fidda gwanin PDP: Ba zan daga wa kowa kafa ba, Gwamna Bala Mohammed

  • Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce babu wani dan takarar da zai daga wa kafa ko ya janye saboda shi a zaben fidda gwanin PDP
  • Ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Asabar inda ya sanar da cewa nasarorin da ya samu a FCT da Bauchi kadai abun dubawa ne
  • Ya sanar da cewa, shi shugaban kasar Najeriya zai zama ba wai shugaban kasar arewa maso gabas ba koda na tsayar dan takarar yarjejeniya

Bauchi - Gwamnan jihar Bauchi kuma dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar PDP, Bala Mohammed, ya ce bai shirya janyewa saboda kowanne dan takarar PDP ba.

Gwamnan ya bayyana matsayarsa ne yayin tattaunawa da Arise TV a ranar Asabar kan yuwuwar bayyanar dan takarar yarjejeniya daga arewa maso gabashin kasar nan a gagarumin taron zaben fidda gwanin da ake yi a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Zaben fidda gwanin PDP: Ba zan daga wa kowa kafa ba, Gwamna Bala Mohammed
Zaben fidda gwanin PDP: Ba zan daga wa kowa kafa ba, Gwamna Bala Mohammed. Hoto daga dailytust.com
Asali: UGC
Ya ce, "Ba zan daga wa kowa kafa ba. Ba shugaban kasan arewa maso gabas zan zama ba, shugaban kasar Najeriya zan zama. Babu wanda zan bi baya cikin 'yan takara na arewa maso gabas. Kalla duk abubuwan da nayi. Na bi tudu, na bi gangare. Na fahimci banbance-banbance.
"Kuma daga daya bangare na mutanen kasar nan da ke Kudu, ku yarda da ni, saboda abinda na yi na kwazo, abubuwan da nayi a babban birnin tarayya, Bauchi da ko na. Don haka. babu wanda zia zo ya ce in daga wa wani kafa."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP

A wani labari na daban, jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata batun dage babban taronta da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, 28 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Batun fitar da dan takarar maslaha ya rushe: Atiku, Saraki da sauran yan takarar PDP sun ce sai an fafata

Gabannin babban zaben 2023, deleget din PDP sun taru a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar inda ake sanya ran taron zai gudana.

Akwai rahotannin cewa babbar jam’iyyar adawar kasar na iya dage zaben fidda dan takararta na shugaban kasa, awanni bayan jam’iyyar APC ta mayar da nata zuwa 6 ga watan Yuni.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, babban sakataren jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar bata tunanin dage taronta zuwa wani rana, Channels TV ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel