Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP

Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP

  • Jam’iyyar PDP a ranar Asabar, 28 ga watan Mayu, ta tabbatar da cewar zaben fidda dan takararta na shugaban kasa zai gudana kamar yadda aka tsara
  • Mai magana da yawun PDP, Debo Ologunagba, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar yayin da yake martani ga ikirarin cewa za su dage babban taronsu
  • Ologunagba ya bayyana cewa tuni suka fara taron nasu sannan ya bukaci jama’a da su yi watsi da rahoton

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta karyata batun dage babban taronta da aka shirya gudanarwa a yau Asabar, 28 ga watan Mayu.

Gabannin babban zaben 2023, deleget din PDP sun taru a Abuja, babbar birnin tarayyar kasar inda ake sanya ran taron zai gudana.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

Akwai rahotannin cewa babbar jam’iyyar adawar kasar na iya dage zaben fidda dan takararta na shugaban kasa, awanni bayan jam’iyyar APC ta mayar da nata zuwa 6 ga watan Yuni.

Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP
Ba mu dage zaben fidda dan takarar shugaban kasa ba - PDP Hoto: Douye Diri
Asali: Facebook

Sai dai a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, babban sakataren jam’iyyar na kasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar bata tunanin dage taronta zuwa wani rana, Channels TV ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta ce a yanzu haka taron nata na gudana kamar yadda aka tsara sannan ta yi kira ga mambobinta da su yi watsi da labarin dage taron, The Cable ta rahoto

Sanarwar ta ce:

“Don kore duk wani shakku, PDP ta bayyana a fili cewa ba ta dage babban taronta na 2022 ba. Babban taron kasa na PDP na 2022 yana nan kamar yadda aka tsara a yau Asabar, 28 ga Mayu, 2022 kuma babu wani tunanin na dage zaben.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Babban dan takarar shugaban kasa na PDP daga arewa ya janye daga tseren

“Tuni PDP a matsayinta na jam’iyya mai tsari ta fara tsare-tsare don zabar dan takararmu na shugaban kasa a zaben 2023 daidai da kudirinmu na cetowa da sake gina kasar daga mulkin zalunci.”

A cewarsa:

“PDP ta mayar da hankali ne inda ta sa gaba kuma ba za ta yarda yaudara APC wadanda ke da burin kitsa rashin tabbas, da kawo cikas ga tsarin zaben ya dauke mata hankali ba."
“APC na fafutukar da babu nasara ne don haka ta yanke shawarar juya lamura kuma wannan makarkashiya nata ba zai taba sanya 'yan Najeriya su yi watsi da kudurinsu na fitar da APC daga mulki ba a 2023 da kuma fara sake gina kasarmu a kan turbar PDP."

Ana wata ga wata: PDP ta kira taron gaggawa, tana duba yiwuwar dage zaben fidda gwaninta

A gefe guda, mun ji a baya cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta kira wani taron gaggawa na shugabanninta na kasa a kokarinta na duba batutuwan gaggawa da suka taso, ciki har da yiwuwar sake dage babban taronta na kasa da aka shirya yi a yau.

Kara karanta wannan

Zaɓen Fidda Gwanin APC: Da Ƙyar Na Sha, Dole Na Tsere Don Kada a Kashe Ni, In Ji Ɗan Majalisa

Ana sanya ran taron na kwamitin NWC wanda ke gudana yanzu haka a Abuja zai magance lamuran da suka shafi shawarar da hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta yanke na tsawaita wa'adin kammala zaben fidda gwani na jam'iyyu a fadin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel