Zaɓen Fidda Gwani: An Kashe Mutum 2 Yayin Rikicin Da Ya Ɓarke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaɓen APC a Legas

Zaɓen Fidda Gwani: An Kashe Mutum 2 Yayin Rikicin Da Ya Ɓarke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaɓen APC a Legas

  • Akalla mutane biyu ne su ka halaka bayan rigima ta barke a wurin da aka yi zaben fidda gwanin APC na majalisar wakilai a Alimosho da ke Jihar Legas
  • Muftau Ogunlaye da Suraju Dauda ne su ka rasu kamar yadda ‘yan sanda su ka tabbatar yayin da mutane da dama su ka samu raunuka
  • A ranar Juma’a da yamma ne wani bidiyo ya bayyana wanda aka ga mutane su na tserewa yayin da ake ta jin harbe-harbe

Legas - Sakamakon zaben fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi na majalisar wakilai a Alimosho da ke Jihar Legas, mutane akalla guda biyu ne su ka rasa rayukansu, Daily Trust ta ruwaito.

Mutane da dama sun raunana, kuma rahotanni sun nuna cewa Muftau Ogunlaye da Suraju Dauda ne wadanda su ka rasa rayukansu.

Kara karanta wannan

Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas

Zaben Fidda Gwani: An Kashe Mutum 2 Yayin Rikicin Da Ya Barke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaben APC a Legas
An Kashe Mutum 2 Yayin Rikicin Da Ya Barke Bayan Sanar Da Sakamakon Zaben Fidda Gwanin APC a Legas. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani bidiyon da ya bazu na lamarin da ya faru ranar Juma’a da yamma, an ga mutane su na ta tserewa don tsira daga harbe-harben da ake ta yi a iska.

Akwai wani bidiyo na daban wanda ya nuna wani mutum kwance cikin jini, da alamu ba ya da rai.

Majiyoyi sun ce mutane 4 aka halaka, amma ‘yan sanda sun tabbatar da mutuwar mutane 2

Sai dai majiyoyi sun bayyana cewa mutane hudu ne su ka rasu yayin da ‘yan sanda su ka tabbatar da mutuwar mutane biyu.

Jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya sanar da wakilin Daily Trust cewa rikicin ya barke ne bayan an sanar da sakamakon zaben.

A cewarsa:

“Mutane biyu sun rasu. Akwai Muftau Ogunlaye mai shekaru 44 da Suraju Dauda, mai shekaru 42. Kawo yanzu dai babu wanda aka kama.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

“An yi zaben fidda gwani ne a yankin. Bayan sanar da sakamakon ne fada ya hautsine.”

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

A wani rahoton, dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.

A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel