Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC

  • Sha’aban Sharada, dan takarar gwamnan Jihar Kano, karkashin jam’iyyar APC ya bayyana dalilinsa na barin wurin zaben fidda gwani, kuma ya ki amincewa da sakamakon
  • Sharada ne kadai dan takarar da ya kalubalanci gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasiru Gawuna a matsayin dan takarar da gwamna ya marawa baya a farkon watan Mayu
  • Sharada ya saki wata takarda a ranar Juma’a wacce ya ce dakyar shi da wasu masu mara masa baya su ka tsira saboda an kusa kai musu farmaki a kuma halaka su

Kano - Dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar APC, Sha’aban Sharada, ya bayyana dalilinsa na barin inda ake zaben fidda gwanin jam’iyyar APC, kuma ya kalubalanci sakamakon zaben.

Sharada ne dan takara daya da ya nuna rashin amincewarsa akan gabatar da mataimakin gwamnan jihar, Nasir Gawuna, a matsayin dan takarar gwamna a farkon watan Mayu, rahoton The Cable.

Kara karanta wannan

Sokoto: Ƴan Takarar APC Sun Fice Daga Wurin Zaɓen Fidda Gwani a Fusace Bayan Ɗaukewar Wutar Lantarki

Kano: An Yi Yunƙurin Kashe Ni Yayin Zaɓen Fidda Gwani, Ban Yarda Da Zaɓen Ba, Ɗan Takarar Gwamnan APC
Sha’aban Sharada ya ki amincewa da sakamakon zaben fidda gwanin gwamnonin APC, ya ce an yi yunkurin halaka shi. Hoto: The Cable.
Asali: Twitter

A wata takarda wacce Daily Nigerian ta saki ranar Juma’a, Sharada ya ce dakyar shi da wasu mabiyansa su ka sha daga harin da aka kai musu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sharada ya ce an ja kunnensa akan zuwa wurin zaben

Kamar yadda ya ce:

“Dakyar na sha yayin da ake zaben fidda gwanin gwamnonin da aka yi yau a Kano. Ana saura mintoci kadan a fara zaben, wani jami’in tsaro ya ja kunne na akan zuwa wurin da ake zaben. Daga nan shugaban kwamitin zaben fidda gwanin jam’iyyar, Sanata Tijjani Kaura ya tura min sako inda ya bukaci in je wurin.
“Abinda ya ba ni mamaki shi ne yadda aka dakatar da jami’an tsaron da aka turo tun daga Abuja raka ni wurin da za a yi zaben. Daga nan wani ya sanar da ni cewa ana ta yada batun yunkurin halaka ni saboda kada in lashe zaben. Hakan ya sa na dauki matakan tsaro na shiga wurin zaben, ina godiya ga Allah (SWT).

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Umar Bago ya lashe zaben fidda dan takarar gwamnan APC a Neja

“A jawabin da na yi, na ja hankalin duk masu ruwa da tsaki akan shirin gwamnatin Jihar Kano na tilasta dan takara ga jam’iyyarmu, inda na shawarci wakilai da su yi amfani da ‘yancinsu da kundin tsarin mulki ya ba su na zaben wanda su ke so. Ba a yi zabe ba.”

A cewarsa, yayin da ake tsaka da zaben, an ci gaba da shirye-shiryen kai masa farmaki, ana so a halaka shi da zarar ya bar wurin.

Daga baya ya kara samun bayani akan yadda aka halaka wasu masu mara masa baya tare da ji wa wasu raunuka wanda hakan ya sa ya yi gaggawar barin wurin su ka zarce asibiti don a duba lafiyarsu.

Ya nemi jami’an tsaro su yi bincike akan kashe-kashen

Ya ce a wurinsa rayuwar mutum daya ta fi masa muhimmanci akan zama gwamna. Hakan ya sa ya yi kira ga jami’an tsaro akan yin bincike mai zurfi tare da hukunta wadanda su ka yi wannan aika-aikar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: APC ta sanar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin gwamna a bauchi

Ya kuma yi kira akan a rushe zaben fidda gwanin da aka ce an yi, don bai nuna nagartar babbar jam’iyya irin APC ba kuma ba haka demokradiyya ta ke ba.

Ya yi wa wadanda su ka rasa rayukansu fatan samun rahamar Ubangiji tare da yi wa marasa lafiyar da su ka samu raunuka fatan samun lafiya.

Buratai: Tsohon Babban Hafsan Sojojin Ƙasan Najeriya Ya Ba Wa APC Gudunmawar Motar Kamfen Ƙirar Najeriya

A wani rahoton, tsohon babban hafsan sojin kasa kuma Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, Janar Tukur Buratai; Babban Kwamishinan Najeriya a Jamhuriyar Zambia, Nwanebike Oghi da kuma wasu jakadu na musamman a ranar Laraba sun bai wa shugabancin jam’iyyar APC kyautar motoci kirar bas mai daukar mutum 18.

Farar motar, wacce kamfanin Innoson Motors ne ya kerata sabuwa ce kuma a jikinta a rubuta “Jakadu na musamman ne su ka bayar da kyautarta,” The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yadda wasu Gwamnonin jihohi su ka yi kutun-kutun har sai da Peter Obi ya hakura da PDP

Sun gabatar da motar ne a babban ofishin jam’iyyar da ke Abuja bayan wakilan sun yi taron sirri da shugaban jam’iyyar, Sanata Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel