Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas

Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas

  • An bayyana mutanen da ke aiwatar da ayyukan ta’addanci ciki harda kashe-kashen bayin Allah da basu ji basu gani a a yankin kudu maso gabas
  • Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ne ya bayyana su a yayin da yake saka dokar kulle a jiharsa
  • Soludo ya bayyana cewa ‘yan bindigar da ba a san ko su waye ba, ba kowa bane face yan Igbo da ke son kafa addininsu na bautar dodanni a yankin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Anambra - Gwamna Charles Soludo na jihar Anambra ya ce yawancin yan bindigar da ba a san ko su waye ba da ke haddasa rikici a jihar yan Igbo ne.

Da yake magana yayin da yake saka dokar kulle a kananan hukumomi bakwai na jihar, Soludo ya yi Allah wadai da ayyukan masu haddasa fitinan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Anambra: Osinbajo ya yi martani kan kisan 'yar Arewa da 'ya'yanta 4 a jihar Kudu

Ya ce dokar kullen zai ci gaba da aiki har sai zaman lafiya ya dawo.

Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas
Inyamurai ne: Gwamna ya bayyana masu hallaka mutane a yankin Kudu maso Gabas Hoto: The Cable
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bari mu fito fili mu fadi gaskiya. Wadannan miyagu da ke haddasa tashe-tashen hankula a Anambra, ’yan kabilar Igbo ne (mafi akasari daga wasu jihohin Kudu maso Gabas) wadanda ainihin manufarsu ita ce aikata ta’asa da tursasa addininsu na bautar dodo a yankin.
“Abun takaici, kowasu guggun masu laifi (ciki harda kungiyoyin asiri) suna ikirarin su masu fafutukar yanci ne, wanda hakan yasa an kasa tantance masu fafutuka na gaskiya da miyagu. Wani abun takaicin kuma shine miyagun sun mamaye koina a yanzu.”

A cewarsa, Anambra aka fi kaiwa hari saboda ita ce wurin da aka fi samun riba wajen garkuwa da mutane don kudin fansa a kudu maso gabas.

Ya ce duk da suna ikirarin cewa “mutane suke yiwa fafutuka” sai gashi suna kashe wadannan mutanen, suna lalata hanyar samun abincinsu sannan suna hana yaransu zuwa makaranta.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

“Wani alaka ne ke tsakanin fafutuka da garkuwa da mutane ciki harda sace malaman addinin Allah, kai farmaki cocina da wuraren bauta tare da yin batanci ga fadin Ubangiji? Me yasa duk inda suka hadu da kuma duk sansanin da suke aiki sai an ga dodanni wanda suke bawa jini?
“Daga abun da wadanda aka sace sannan aka saki suke fadi sun ce akwai tarin gawawwaki a sansanonin. Mun ga bidiyonsu da bautar dodanni da suke yi; mun lura da barazanarsu ga limamai da manyan fastoci, ciki harda barazanar kwace wasu cocina.”

Ya kuma bayyana cewa an san Igbo da harkokinsu na kasuwanci amma wadannan miyagu sun karkata wajen kashe kasuwancin Igbo ya hanyar tursasa dokar zaman gida da haramtaciyyar kungiyar IPOB ke yi.

Ya ci gaba da cewa:

“Mutanen kudu maso gabas musamman Anambra, kiristoci ne. Amma da wannan guggun mutanen, bautar dodanni ya dawo. Suna kokarin mayar da mutane musamman matasa masu bautar dodanni ta hanyar saka su a kungiyoyin asiri, suna daukar rantsuwa ga doddaninsu da alkawara. Don haka wadannan matasa na shiga cikinsu a matsayin mambobi da masu yi masu kwarmato.

Kara karanta wannan

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

“Bisa al’adarmu: zubar da jinin bayin Allah da basu ji ba basu gani ba haramun ne a al’adarmu da addininmu na kirista. Mun fahimci cewa suna kashewa da cire sassan jikin yan Adam don yin tsafi a sansanoninsu.
“Da wannan sabuwar addini nasu na bautar gumaka da muggan makamai da suke amfani da shi wajen kashe mutane, sun yi kokarin kafa al’adar tsoro da shiru. A yan baya-bayan nan, mutane sun fara dasa ayar tambaya kan farfagandarsu, manufa da hanyoyinsu kuma sun san cewa mutane sun daina tausaya masu.
"Wannan ya bayyana dalilin da yasa suke son haddasa rikicin kabilanci na kasa ta hanyar kashe yan Arewa da basu ji ba basu gani ba wadanda ke zaman lafiya a jiharmu tsawon shekaru masu yawa don kawar da idanu kan ta’asar da suke aikatawa sannan su lullube kansu a matsayin masu kare mutane.”

A cewar Soludo, sun gaza kuma za su ci gaba da gazawa.

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

Kisan gillan da IPOB suka yiwa Bahaushiya da 'ya'yanta 4: Gwamnan Anambra ya ce ba Hausawa aka nufi farmaka ba

A gefe guda, mun ji a baya cewa Gwamna Chukwuma Soludo na jihar Anambra ya bayyana cewa ba yan arewa ake nufin kashewa ba a jihar.

Soludo ya bayyana hakan ne yayin da yake martani ga kisan wata mata mai ciki da yaranta da wasu da ake zaton yan awaren IPOB ne suka yi, Daily Trust ta rahoto.

A cikin wata sanarwa daga Mista Christian Aburime, babban sakataren labaransam Soludo ya ce yan asalin Anambra, yan arewa da mutane daga sauran yankunan kasar suna zama tare da yin kasuwanci da juna cikin lumana, rahoton Daily Post.

Asali: Legit.ng

Online view pixel