An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa, Hotuna

  • Yayinda ake tsaka da gudanar da zaben fidda gwnain gwamnan APC a jihar Adamawa, yan sanda sun kai simame
  • An damke wasu sankame da makudan kudade suna shirin rabawa Delegete don zaben daya daga cikin ya takara
  • Abin mamaki shine yayinda aka ga hotunan Sanata Aishatu Dahiru Binani cikin jakar kudaden

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Yola - An damke wasu yan siyasa biyu da ake zargin masu yiwa Sanata Aisha Binani yakin neman zabe ne suna rabawa Deleget makudan kudi a jihar Adamawa.

Aisha Binani, wacce Sanata ce mai wakiltar mazabar Adamawa ta tsakiya a yanzu tana neman zama gwamnan jihar.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa Sanatar ta yiwa Deleget alkawarin basu ninkin duk kudin da sauran yan takara suka basu.

An tattaro cewa sun fara tuntubar Deleget kenan don raba musu kudi yayinda aka fara zaben fidda gwanin dake gudana da daren nan.

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

An damkesu ne misalin karfe 8 na dare yayinda jami'an tsaro suka dira wajen da ake rabon kudi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Rahoton ya kara da cewa tuni an garzaya da su ofishin CID na yan sanda tare da kudaden

An tuntubi Sanata Binani don jin ta bakinta ba ta ki daga waya.

Kalli hotunan:

Yaran siyasan Aisha Binani
An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa Hoto: DailyNigerian
Asali: Facebook

An damke yaran siyasan Aisha Binani suna rabawa Deleget makudan kudi a Adamawa

2023: Sanata Aisha Binani za ta nemi takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC

A baya mun kawo muku cewa Sanata Aishatu Dahiru Ahmed wanda aka fi sani da Binani, ta bayyana shirinta na neman takarar kujerar gwamna a zabe mai zuwa.

Daily Trust ta fitar da rahoto a ranar Laraba, 16 ga watan Maris 2022, inda aka ji Aishatu Dahiru Ahmed tana harin kujerar gwamnar jihar Adamawa.

Sanata Aishatu Ahmed ta sanar da Duniya hakan ne a ranar Talata a lokacin da ta ziyarci sakatariyar jam’iyyar APC a birnin Yola, jihar Adamawa.

Kara karanta wannan

Fito na fito da Gwamna Bagudu: Adamu Aliero ya janye daga neman kujerar Sanata

Sanatar ta Adamawa ta tsakiya ta yi wa ‘ya ‘yan jam’iyyar hamayyar alkawari cewa idan ta lashe zaben gwamna a 2023, za ta kawo sauyi a Adamawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel