Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party

Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party

  • Tsohon abokin tafiyar Atiku a zaben 2019, Peter Obi, ya koma jam'iyyar yan kwadago
  • Peter Obi yace ya fita daga PDP ne saboda abubuwan da ake a wajen sun sabawa nagartarsa
  • Dan siyasan yace yanzu zai yi takarar kujeran shugaban kasa karkashin sabuwar jam'iyyarsa

Anambra - Tsohon Gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, wanda yayi murabus daga jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ranar Laraba ya koma jam'iyyar Labour Party (LP).

Peter Obi ya koma LP don takara kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Peter Obi ya yi rijista matsayin mamban jam'iyyar ranar Juma'a a gundumarsa dake Anambra.

Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party
Yanzu-yanzu: Bayan fita daga PDP, Peter Obi ya koma jam'iyyar Labour Party Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

Peter Obi da kansa ya bayyana hakan da yammacin Juma'a a shafinsa na Tuwita.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Sunayen jihohi da 'yan takarar gwamnoni da suka yi nasarar samun tikitin APC a zaben fidda gwani

A jawabin da ya fitar, yace:

"Tun da nayi murabus daga PDP saboda wasu abubuwa da suka sabawa ka'idoji na, na nemi shawara da jam'iyyu da dama da mutane don tabbatar da cewa bamu bata ba."
"Saboda haka, na zabi wata hanyar da nike ganin tayi muwafaqa da bukatu ne don dauke kasar nan daga ci-mu-ci zuwa samar da abinci; kuma itace jam'iyyar Labour Party."

Wike ya caccaki Obi

Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya caccaki Peter Obi kan fitarsa daga jam'iyyar PDP.

Da aka yi hira da shi, an rahoto Nyesom Wike yana cewa Peter Obi ba zai lashe zaben zama ‘dan takarar shugaban kasa ba ko da ya yi zamansa a PDP.

Da yake magana a ranar Alhamis, Premium Times ta ce gwamnan na Ribas ya ce bai yi mamakin matakin da tsohon gwamnan na Anambra ya dauka ba.

Wike ya ce tun da Obi ya sauka daga kujerar gwamnan Anambra a APGA, bai sake cin zabe a jihar ba, ya soki yunkurinsa na neman mataimaki a NNPP.

Kara karanta wannan

DG: Peter Obi ba zai shiga NNPP, su yi takara tare da Kwankwaso a zaben 2023 ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel