Zaben fidda gwanin PDP: Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa

Zaben fidda gwanin PDP: Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta fara gudanar da zaben fidda yan takararta na mukamai daban-daban a babban zaben 2023.

A halin yanzu, wasu gwamnoni da za su kammala wa’adinsu na biyu a 2023 sun yi nasarar mallakar tikitin takarar zaben sanata. Wasu mataimakan gwamnoni ma sun shiga tseren kujerar sanatan.

Zaben fidda gwanin PDP: Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa
Jerin gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka lashe tikitin majalisar dattawa Hoto: Benue State Government, Governor Darius Dickson Ishaku, Abia State Government, Nigeria, Ifeanyi Lawrence Ugwuanyi
Asali: Facebook

Ga gwamnoni da mataimakan gwamnoni da suka mallaki tikitin takarar majalisar dettawa ta PDP.

GWAMNONI

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue

Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue ya lashe tikitin PDP don takarar kujera a majalisar dattawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Zai daga tutar PDP na sanata mai wakiltan Benue ta arewa maso yamma a zaben 2023.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Ortom ya samu tikitin takarar jam’iyyar ne ba tare da abokin hamayya ba.

Kara karanta wannan

An samu matsala: 'Yan bindiga sun harbe deliget 3 na zaben gwamnan PDP a jihar Arewa

Gwamna Darius Ishaku na jihar Taraba

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ma ya samu tikitin PDP domin takarar kujerar sanata mai wakiltan Taraba ta kudu.

Idan ya yi nasara a babban zaben 2023, Ishaku zai shiga jerin gwamnonin da suka koma majalisar dokokin tarayya bayan kammala shekaru 8 a shugabancin jaharsu.

Gwamna Okezie Ikpeazu na jihar Abia

Hakazalika, an zabi gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu a matsayin dan takarar sanata mai wakiltan Abia ta kudu ba tare da abokin hamayya ba.

Ikpeazu wanda shi daya tilo ne dan takara a zaben ya samu kuri’u 198.

Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu

Gwamna Ifeanyi Ugwuyi na jihar Enugu ma ya yi nasarar samun tikitin PDP na sanata mai wakiltan Enugu ta arewa.

An kaddamar da Unguanyi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin da ya gudana a ranar Talata, 24 ga watan Mayu, a filin wasa na Nsukka da ke karamar hukumar Nsukka ta jihar, Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

Da yake sanar da sakamakon, jami’in zabe, Yandev Ammabai, ya ce Unguanyi ya samu kuri’u 299 wajen kayar da abokin hamayyarsa, Eze Godwin wanda ya samu kuri’u 16 yayin da Godsmack Ugwu da Okanye Celestine basu samu komai ba.

MATAIMAKAN GWAMNONI

Harry Banigo

Mataimakiyar gwamnan jihar Rivers, Dr Misis Ipalibo Harry Banigo ta lashe tikitin PDP a zaben fidda dan takarar gwamna mai wakiltan Rivers ta yamma.

Banigo ta lashe zaben fidda gwanin ba tare da abokin hamayya ba a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu.

Haruna Manu

Mataimakin gwamnan Taraba, Injiniya Manu, ya lashe tikitin PDP na yankin Taraba ta tsakiya.

Mataimakin gwamnan da yake magana bayan nasararsa, ya sha alwashin cewa ba zai baiwa mutanen yankinsa kunya ba idan ya yi nasara a zaben na 2023.

Tsayar da dan takarar shugaban kasa: Shugaban APC ya magantu, ya ce ba lallai a samu harshe daya ba

A wani labarin, gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), wanda za a fara a ranar Lahadi, shugaban jam’iyyar na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ba lallai bane tsarin maslaha da aka yi amfani da shi wajen zaban shugabannin jam’iyyar a watan Maris ya yi aiki.

Kara karanta wannan

Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP

A wata hira da ya yi da muryar Amurka a Abuja a ranar Laraba, 25 ga watan Mayu, Adamu ya ce zaben fidda dan takarar shugaban kasa ya sha banban sosai da na zaben shugabancin jam’iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng