Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP

Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP

  • Siyasar PDP dai na ci gaba da daukar wani salo mai jan hankali, ana ci gaba da samun dirkaniya a wasu jihohin
  • Dan takarar gwamna a jihar Sokoto ya yi saraf ya fice daga PDP saboda wasu dalilai na siyasa da ba su mishi dadi ba
  • Hakazalika, rahoton da muke samu ya bayyana cewa, dan takarar ya yi baram-baram da gwamna mai ci a jihar Sokoto

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Sokoto - Wani babban jigon jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Sokoto, Mukhtari Shehu Shagari, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.

Dan siyasar na daya daga cikin manyan yan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar ta PDP.

Siyasar jihar Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP
Sokoto: Dan takarar gwamna ya yi baram-baram da Tambuwal, ya fice daga PDP | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Shagari, wanda ya kasance tsohon ministan albarkatun ruwa na jihar Sokoto kuma tsohon mataimakin gwamna ya sanar da ficewarsa jim kadan bayan taron masu ruwa da tsaki da jam’iyyar da aka yi.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Bayan janyewa daga takarar shugaban kasa, Peter Obi ya fice daga PDP

Taron wanda Gwamnan jihar ya jagoranta ya tsayar da tsohon sakataren gwamnatin jihar a matsayin dan takarar gwamna na PDP a zabe mai zuwa, jaridar Punch ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shagari a wani jawabi dauke da sa hannunsa, ya zargi gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal da aikata ha’inci.

Ya ce:

“Ina burin sanar da ku cewa Ni, Mukhtari Shehu Shagari daga yau na tashi daga dan jam’iyyar Peoples Democratic Party.
“Wannan hukuncin mai tsauri ya kasance ne sakamakon jerin cin amana da na fuskanta a hannun jam’iyya da ke ikirarin karya cewa tana kan tafarkin damokradiyya amma maimakon haka ta zama jam’iyyar kulla ciniki da wanda ya fi sakin kudi ba tare da la’akari da aiki, jajircewa, sadaukarwa, zuba jari da hidimar da mutum ya yiwa jam’iyyar tun 1998 ba.
“Baya ga tarin sadaukarwar da nayi da hidimtawa jam’iyyar, PDP da ake magana a kanta bata da tsarin sakawa mutum da alkhairi.”

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

Mohammed Abacha ya lashe zaben fidda gwanin PDP na gwamna a Kano

A wnai labarin, Mohammed Abacha, dan marigayi tsohon shugaban kasa, Sani Abacha, ya lashe zaben fidda dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a Kano.

Jami'ar zabe, Barista Amina Garba, ta ayyana Mista Abacha a matsayin wanda ya lashe zabe bayan ya samu kuri’u 736 wajen kayar da babban abokin hamayyarsa, Sani-Bello wanda ya samu kuri’u 710, PM News ta rahoto.

Shugaban kwamitin zaben, Mohammed Jamu, ya ce an gudanar da zaben fidda gwaninsu bisa ka’ida tare da zababbun deleget sannan hukumar zabe ta kasa (INEC), yan sanda da Jami’an DSS suka sanya idanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng