Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

  • Mai martaba Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya nuna goyon bayansa ga kudirin mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo na son gaje Buhari
  • Basaraken ya bayyana cewa suna goyon bayan Osinbajo sannan za su saka shi a addu'a domin rokon Allah ya sa ya zama shugaban kasa a 2023
  • Sarkin ya kuma yaba ma gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda ya ce ya yiwa kasar kokari sosai duk da tarin kalubale

Yobe - Sarkin Damaturu, Hashimi II El-Kanemi, ya bayyana cewa masarautarsa za ta marawa mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo baya tare da saka shi a addu’a don Allah ya daura shi kan kujerar shugabancin Najeriya a 2023.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa sarkin ya dauki wannan alkawarin ne yayin da ya tarbi mataimakin shugaban kasar, wanda ya kai ziyarar ban girma fadarsa da ke Damaturu, babbar birnin jihar Yobe a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023
Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023 Hoto: Yemi Osinbajo
Asali: Facebook

Osinbajo ya ziyarci Yobe don ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin zaben fidda dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Basaraken ya ce ziyarar da mataimakin shugaban kasar ya kai fadar alamu ne da ke nuna yana mutunta sarautar gargajiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Abin da muke tsammani shi ne ci gaba; daurawa a kan abin da aka kafa kuma mun doshi hanyar hakan.
“Don godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari; idan ka kawo maganar tsaro gwamnan mu zai ba da shaida kan abin da ya faru a jihar nan; abun da ya wakana a wannan jihar; amma da Buhari ya hau mulki sai al’amura suka gyaru; abubuwa sun inganta.
“Mun samu zaman lafiya a wannan gwamnati; Shugaba Buhari ya yi wa wannan kasa kokari sosai; yana kokari sosai duk da kalubale; akwai bukatar mu jinjinawa jagorancinku sosai.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

“Da izinin Allah za mu saka ka a addu’o’inmu sannan za mu mara maka baya a dukkan bangarori don ganin cewa ka yi nasara, kuma a karshe muna addu’a cewa Allah ya sa ka zama shugaban wannan kasa mai albarka.”

El-kanemi ya yaba wa Gwamna Mai Mala Buni, wanda ya ce ya sadaukar da kansa wajen gudanar da mulkin jihar tare da kulla kyakkyawar alaka da masarautar gargajiya, rahoton Vanguard.

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

A wani labarin kuma, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, ya bayyana cewa yana da dukkan abun bukata domin gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lawan ya bayyana hakan ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja, yayin da yake jawabi ga deleget din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Sarkin Katsina ga Osinbajo: Muna bayanka, Ina addu'ar ka yi nasarar gaje Buhari

Mai neman takarar shugabancin kasar da tawagar kamfen dinsa sun gana da Gwamna Abubakar Sani Bello da deleget na zaben fidda dan takarar shugaban kasa sannan daga bisani suka kai ziyarar ban girma ga Sarkin Minna, Dr. Umar Farouq Bahago.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng