Gombe: Bayan shan kaye a APC a 2018, Barde ya dawo PDP, ya samu tikitin gwamna na 2023

Gombe: Bayan shan kaye a APC a 2018, Barde ya dawo PDP, ya samu tikitin gwamna na 2023

  • A ci gaba da samun rahotannin tattara sakamakon zaben fidda gwani na PDP, Muhammad Jibril Dan Barde ya lashe tikitin PDP a Gombe
  • Wannan na zuwa ne shekaru bayan da dan siyasar ya gaza samun tikitin zaben gwamna na 2019 a karkashin jam'iyyar APC
  • Bayan lashe zaben a yau Laraba, Dan Barde ya magantu da manema labarai, inda ya godewa daukacin masoyansa

Jihar Gombe - Muhammad Jibril Dan Barde ya lashe tikitin takarar gwamna a jam'iyyar PDP a zaben 2023 a jihar Gombe da aka gudanar.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, jami'in zabe, Mista Mike Oghiadomhe, ya ce Barde, ya samu kuri’u 160 inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa, Dr Jamilu Isyaku Gwamna, wanda ya samu kuri’u 119.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamna ya lashe tikitin PDP don sake takarar gwamna a 2023

Dan Barde ya samu nasarar lashe zaben fidda gwani
Gombe: Bayan shan kaye a APC a 2018, Barde ya dawo PDP, ya samu tikitin gwamna na 2023 | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sauran ‘yan takarar, sun hada da AVM Adamu Shehu Usman (rtd) ya samu kuri’u 18, Dakta Abubakar Ali Gombe, da kuri’u 17, Dakta Babayo Ardo Kumo ya samu kuri’u 13, yayin da Dokta Gimba Ya’u Kumo ya samu kuri’u daya tilo.

Dan Barde shi ne wanda ya kafa kuma tsohon manajan darakta kuma babban jami’in bankin Sun Trust, inji rahoton Daily Trust.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shi ne wanda ya zo na biyu a zaben fidda gwani na gwamna a 2018 wanda ya samar da gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2019.

A wani takaitaccen jawabi, Barde ya bayyana sakamakon a matsayin nasara ga ‘ya’yan jam’iyyar PDP a jihar.

Ya kara da cewa lokaci ya yi da za a kori gwamnatin APC a jihar.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Shahararren gwamnan Arewa ya lashe zaben fidda gwani na gwamnan PDP

Jim kadan bayan sanar ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben, Dan Barde ya shaidawa manema labarai, ciki har da Legit.ng Hausa da ke jihar Gombe cewa, yana godiya da irin goyon bayan da ya samu.

Ya kuma bayyana cewa, lallai yanzu ne ya samu damar kawar da jam'iyyar APC da kwamutsenta daga fadar gwamnatin jihar.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa inda ya ce:

"Yanzu muka fara wannan gwagwarmaya, har sai mun samu nasarar samun mulkin jihar Gombe da yardar Allah."

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

A jihar Neja kuwa, jam'iyyar adawa ta PDP ta dage zaben fitdda gwani da ke gudana a jihar Neja, biyo bayan wata zanga-zanga da ta barke, inji rahoton Daily Trust.

Zaben da aka shirya gudanarwa a yau Laraba ya koma Alhamis bayan zanga-zangar da hudu daga cikin biyar da ke takara suka tayar.

Kara karanta wannan

'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP

Rahoto ya bayyana cewa an fara samun matsala ne yayin da hudu daga cikin biyar din suka nuna rashin gamsuwa da jerin sunayen deliget-deliget da za su kada kuri'a, rahoton Premium Times.

Asali: Legit.ng

Online view pixel