'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP

'Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kuɗinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaɓen Fidda Gwanin PDP

  • Bayan samun kuri’u biyu kacal a zaben fidda gwanin jam’iyyar PDP na mazabar Kaduna ta Arewa, Adam Namadi ya nemi wakilan jam’iyyar su mayar masa da kudadensa
  • Adam Namadi dan tsohon mataimakin shugaban kasa ne, Namadi Sambo, kuma an samu rahotanni akan yadda ya ba ko wanne cikin wakilan Naira Miliyan biyu kafin a fara zaben
  • Duk da ya yi alkawarin karawa ko wanne wakili Naira Miliyan 1.5, shi ne dan takarar da ya sami kuri’u mafi karanci yayin da Samaila Suleiman ya lashe zaben

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Dan tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Namadi Sambo, Adam Namadi ya bukaci wakilan jam’iyyar PDP da ya bai wa ko wannensu N2,000,000 su mayar masa da kudadensa da su ka tatsa kafin zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka yi bayan ya samu kuri’u biyu kacal.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa ba zan ba masu tsaida takara a PDP ko sisi ba - Mai neman Gwamnan Kano

Daily Trust ta ruwaito cewa Namadi ya yi alkawarin kara wa wakilan N1,500,000 bayan an kammala zaben, sai dai shi ne ya kasance dan takarar da ya samu mafi karancin kuri’u.

Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kudinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaben Fidda Gwanin PDP
Dan Namadi Sambo Ya Nemi Deliget Su Mayar Masa Da Kudinsa Bayan Ya Sha Kaye a Zaben Cikin Gida na PDP. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga karshe Suleiman ne ya lashe zaben da kuri’u 22

Wakilan jam’iyyar sun samu miliyoyin nairori a hannun ‘yan takarar da su ka nuna matukar burin son lashe zaben fiye da abokan takararsu.

A karshe, Samaila Suleiman, wakilin mazabar ya kayar da Namadi da Shehu Usman ABG.

Daily Trust ta bayyana cewa Suleiman bai dade da sauya sheka daga jam’iyyar APC ba, zuwa PDP, kuma ya samu kuri’u 22, yayin da Shehu Usman ABG ya samu kuri’u 14.

Namadi shi ne wanda ya ba wakilan kudi mafi karanta a cikin ‘yan takarar

Wakilan sun bayyana yadda Suleiman ya rarraba wa ko wannensu Naira miliyan 3.5 zuwa 4 yayin da ABG ya ba su Naira miliyan 2.5, sai kuma Namadi da ya raba wa ko wanne wakili Naira miliyan 2.

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

Amma bayan ABG da Namadi sun sha kaye, Namadi ya bukaci a yi gaggawar mayar masa da kudinsa.

Suleiman, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Ayyuka na Musamman a majalisar, ya bar APC ne bayan babban dan Gwamna Nasir El-Rufai ya nuna yana son kujerarsa.

2023: Tsohuwar Matar Shugaban APC Na Kasa Ta Siya Fom Din Takarar Gwamna a Nasarawa

A wani rahoon, Fatima Abdullahi, tsohuwar matar shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Adamu, ta siya fom din takarar gwamnan Jihar Nasarawa, The Sun ta rahoto.

Za ta tsaya takarar ne don a yi zaben fidda gwani na jihar nan da wata daya, The Punch ta ruwaito.

Yayin da ta ke bayani bayan tuntubar shugabannin APC a ofishin jam’iyyar da ke Lafia, ranar Juma’a, Fatima ta ce ta tsaya takarar ne don gyara akan kura-kuran da wannan mulkin ya yi.

A cewarta, Jihar Nasarawa tana bukatar shugaba mai hangen nesa da kuma jajircewa don ciyar da jihar gaba.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel