2023: INEC ta bayyana mummunar illar da dage zabukan fidda gwani za su a zabe mai zuwa

2023: INEC ta bayyana mummunar illar da dage zabukan fidda gwani za su a zabe mai zuwa

  • Shugaban hukumar INEC na kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a samu mummunar illa matukar aka dinga dage zabukan fidda gwani
  • Kamar yadda ya bayyana ta bakin sakataren yada labaransa, dage zabukan fidda gwani na jam'iyyu zai iya tarwatsa jadawalin zaben 2023 a Najeriya
  • Ya sanar da cewa, a watan Fabrairu da aka fitar da tsarin, babu wata jam'iyya da ta soki hakan, amma har yanzu gashi nan ana fama da su

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta ce dage lokutan zabukan fitar da gwani da jam'iyyun siyasa ke yi idan an bar su zai yi mummunar illa ga zaben shekarar 2023 na kasar nan.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Rotimi Lawrence Oyekanmi, babban sakataren yada labarai na shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya sanar da hakan a ranar Lahadi a Abuja cewa INEC ta bai wa jam'iyyu isasshen lokaci domin yin zaben fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Amma dai tela bai kyauta ba: Dinkin rigar wani yaro ya girgiza intanet, ana ta cece-kuce

2023: INEC ta bayyana mummunar illar da dage zabukan fidda gwani za su a zabe mai zuwa
2023: INEC ta bayyana mummunar illar da dage zabukan fidda gwani za su a zabe mai zuwa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

ThisDay ta ruwaito cewa, ya yi martani ne ga ikirarin wani jigon APC, Gbenga Olawepo-Hashim, wanda ya zargin hukumar da saka tsananin hatsari ga zaben 2023 kan zargin ta da yayi da siyasar bangaranci.

Amma a yayin martani, Oyekanmi ya ce INEC tana da karfin ikon bayar da lokacin da za a yi zaben fidda gwani.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kamar yadda Oyekanmi yace, bukatar dage lokutan zaben fidda gwani idan aka amince, zai lalata tsarin zaben 2023 da aka yi da mummunar illa.

Ya ce, "INEC tana da karfin ikon bada lokacin zaben fitar da gwani, akasin yadda wasu ke kallo. A bayyane yake bai karanta dokokin zabe ba wanda hakan abun kunya ne.
"A lokuta daban-daban har uku, shugaban INEC ya yi kira ga jam'iyyun siyasa da su yi zaben fitar da gwaninsu a cikin lokacin da jadawali ya nuna saboda ba za a sake tsawaita lokaci ba.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

"Idan aka amince da karin lokacin, hakan zai lalata tsarin shirin zaben 2023 wanda hakan zai tabbatar da babbar illa.
"Me yasa jam'iyyun ba za su yi zaben fitar da gwani ba cikin watanni biyu da aka tsara? Abun mamaki, babu wanda ya yi korafi kan jadawalin lokacin da INEC ta fitar a watan Fabrairu. Me yasa sai yanzu?"Ya tuhuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel