Wani ɗan takara a jam'iyyar PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye da zaɓen fidda gwani

Wani ɗan takara a jam'iyyar PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye da zaɓen fidda gwani

  • Ɗan takarar kujerar majalisar wakilai ta ƙasa a jihar Delta, Philip Okwuada, ya sume bayan jin yadda ta kaya a zaɓen fidda gwani
  • Bayanai sun nuna cewa ɗan siyasan ya samu tabbacin samun nasara kafin zaɓen amma Deleget suka yaudare shi ya sha ƙasa
  • A halin yanzun ya samu sauki kuma ya dawo hayyacinsa, ya koma gida ya na hutawa

Dalta - Ɗan takarar kujerar majalisar wakilan tarayya karkashin inuwar PDP, Dakta Philip Okwuada, a ranar Litinin, ya yanke jiki ya faɗi sumamme bayan shan kaye a zaɓen fidda gwani a jihar Delta.

Wakilin Punch ya tattaro cewa Mista Okwuada, wanda ya shiga neman tikitin takarar ɗan majalisa mai wakiltar Ika a majalisar dokokin tarayya, ya faɗi ne yayin da yake hira da yan jarida jim kaɗan bayan sanar da sakamako.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun buɗe wa jerin gwanon motocin wani ɗan takarar APC wuta, sun halaka da dama

Taswirar jahar Delta.
Wani ɗan takara a jam'iyyar PDP ya yanke jiki ya faɗi bayan shan kaye da zaɓen fidda gwani Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Okwuada ya samu kuri'u Bakwai kacal daga kuri'un da aka kaɗa a zaɓen, yayin da wanda ya samu nasara Victor Nwokolo, ya samu kuri'u 75.

Wata majiya daga yankin ta shaida wa jaridar ranar Talata cewa ɗan siyasan ya kaɗu sosai duba da yaƙini da alƙawarin da aka mi shi kafin ranar zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyar ta ce:

"Ɗan uwa na, tabbas abun ya faru kuma gaskiya ne mutumin ya faɗi sumamme, ya kaɗu har ta masa yawa kuma wannan ne karo na uku da ya nemi tikitin kujerar."
"Ya nemi takarar ɗan majalisar jiha tun a 2009 amma bai ci nasara ba. Tun daga 2015 yake neman takarar ɗan majalisar tarayya har zuwa yau kuma be samu ba. Ka duba nisan, kuri'u 7 ya samu, wanda ya ci kuma 75."

Wane hali ya shiga bayan sumewar?

Kara karanta wannan

Bayan kokarin sulhu, Gwamna ya shata layin yaƙi da yan bindiga, ya ce zai hana su sakat

Game da halin da ɗan siyasan ke ciki bayan faruwar lamarin, majiyar ta kara da cewa, "Zan iya cewa ya dawo hayyacinsa, yanzu haka yana gida yana hutawa."

A wani labarin kuma EFCC ta ayyana neman Akanta Janar da wasu manyan Jami'an gwamnati ruwa a jallo kan N435bn

Hukumar yaƙi da cin hanci EFCC ta ayyana neman Akanta Janar na jihar Ribas da wasu mutane kan ɓatan wasu kudi kimanin biliyan N435bn.

Hukumar ta yi kira ga yan Najeriya da su taimaka mata da sahihan bayanai wajen cafke waɗan da ake zargi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel