Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina

  • Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da harin yan bindiga a kan kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia
  • Ta bayyana cewa mutane 12 sun rasa ransu a harin yayin da yawancinsu ke kokarin tserewa cikin gonakinsu
  • Kakakin rundunar, SP Gambo Isah ya ce kwamishinan yan sandan jihar ya jagoranci tawagar tsaro zuwa yankin don ganin halin da ake ciki

Katsina - Tsagerun yan bindiga sun kashe akalla mutane 12 a kauyen Gakurdi da ke karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina, Channels TV ta rahoto.

Yan ta’addan sun kona gonaki da dama mallakar mazauna kauyen a yayin farmakin sassafe da suka kai yankin wanda ya shafe tsawon awanni.

Wani ganau ya shaidawa gidan talbijin na Channels cewa maharan dauke da muggan makamai sun isa kauyen ne a kan babura sannan suka fara harbi kan mai uwa da wabi don tarwatsa al’ummar garin.

Kara karanta wannan

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

Hakan ya haifar da rudani a kauyen, lamarin da ya sanya mazauna neman mafaka a garuruwan da ke makwabtaka.

Rundunar yan sandan jihar ta yi martani

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da faruwar al'amarin a yau Talata, 24 ga watan Mayu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin yan sandan jihar, SP Gambo Isah, da yake tabbatar da faruwar lamarin, ya ce daga cikin wadanda abun ya ritsa da su akwai mazauna kauyen da suka yi kokarin tserewa cikin gonakinsu, jaridar Punch ta rahoto.

Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina
Rundunar yan sanda ta tabbatar da kisan mutum 12 a wani harin sassafe da yan bindiga suka kai Katsina Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa tuni jami’an tsaro suka hau kan lamarin yayin da kwamishinan yan sandan jihar, Idris Dauda Dabban ya jagoranci tawagar tsaro zuwa kauyen don gani da ido.

Isah ya ce:

“Eh, da gaske ne, lamarin ya afku. Yan bindigar sun farmaki kauyen da safiyar yau Talata sannan sun kashe mazauna kauyen 12.”

Kara karanta wannan

Fusatattun mutanen gari sun lakaɗawa wani da dubunsa ta cika dukan tsiya har Lahira a Katsina

“Wasu daga cikin mutanen da aka kashe sun hada da wadanda suka yi kokarin tserewa zuwa gonakinsu.
“Kwamishinan yan sanda, CP Idris Dauda Dabban ya jagoranci wata tawaga ta jami’an tsaro zuwa kauyen da safen nan.”

Kuma dai: ‘Yan bindiga sun farmaki ofishin yan sanda a Anambra, sun kona motoci

A wani labari na daban, mun ji cewa bayan kashe mutane bakwai da suka yi a jiya Lahadi, 22 ga watan Mayu, tsagerun 'yan bindiga sun sake kashe wasu mutum hudu a wurare biyu a jihar Anambra.

Maharan sun kuma farmaki wani ofishin yan sanda a garin Anaku da ke karamar hukumar Ayamelum sannan suka kona motocin da ke wajen, Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel