Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari

  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ziyarci jihar Neja domin zawarcin kuri’un deleget na APC gabannin zaben fidda gwanin jam’iyyar
  • Lawan ya bayyana cewa shine yake da da dukkan abun bukata domin gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari
  • Mai neman shugabancin kasar ya ce yana da kayan aiki, kwarewa da gogewar da ake bukata domin jagorantar kasar a 2023

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Niger - Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan a ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, ya bayyana cewa yana da dukkan abun bukata domin gaje kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Lawan ya bayyana hakan ne a garin Minna, babbar birnin jihar Neja, yayin da yake jawabi ga deleget din jam’iyyar All Progressives Congress (APC) daga jihar, jaridar The Nation ta rahoto.

Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari
Shugaban majalisar dattawa: Ni na ke da duk abin da ya dace na gaje kujerar Buhari Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Ya ce:

“Ina da kayan aiki. Ina da kwarewa sosai, ina da abin da ake bukata don zama shugaban kasa bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya bar mulki."

Kara karanta wannan

Sabon rikici ya kunno kai a APC reshen Kaduna, surukin Buhari bai aminta da deleget din jam’iyyar ba

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mai neman takarar shugabancin kasar da tawagar kamfen dinsa sun gana da Gwamna Abubakar Sani Bello da deleget na zaben fidda dan takarar shugaban kasa sannan daga bisani suka kai ziyarar ban girma ga Sarkin Minna, Dr. Umar Farouq Bahago.

A cewar wani jawabi daga mai bashi shawara na musamman kan harkokin labarai, Ola Awoniyi, ya nemi kuri’un deleget din bisa la’akari da abubuwan da yake son yi, tarin gogewarsa a bangaren shugabanci da kuma zaman lafiyar da ya kawo wa majalisar.

Gwamna Bello ya godewa shugaban majalisar dattawan da tawagarsa bisa ziyarar da suka kawo masu, rahoton Vanguard.

Ya ce:

“Ina tsammanin ya gabatar maku da tsare-tsarensa ga jihar Neja domin ku deleget ku duba, ta yadda za ku bashi kuri’unku don ya wakilci jam’iyyarmu a zaben shugaban kasa na gaba.

Kara karanta wannan

Sarkin Damaturu ga Osinbajo: Muna addua'ar Allah yasa ka gaji Buhari a 2023

“Bana bukatar magana da yawa. Duk kun ji a lokacin da ya fara. Ya kasance a majalisar dokokin tarayya tun 1999. Bana tunanin wani ya kafa wannan tarihin tukuna a Najeriya.”

Yana Sanatan APC amma sunan Danjuma Goje ya bayyana wajen zaben fidda gwanin PDP

A wani labarin, wakilan zaben shugaba wadanda akafi sani da deleget na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Gombe sun ga abin mamaki ranar Litnin wajen zaben fidda gwani.

Yayinda suka shiga kada kuri'unsu, sai suka ga Sanatan APC mai wakiltar Gombe ta tsakiya, Danjuma Goje, cikin jerin yan takaran, rahoton Leadership.

Zaku tuna cewa an yi rade-radin Sanata Danjuma Goje zai sauya sheka daga APC zuwa PDP sakamakon rashin jituwar dake tsakninsa da Gwamnan jihar, Muhammad Inuwa Yahaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel