Mutum 5 kacal ke neman takarar shugaban Najeriya tsakani da Allah inji ‘Dan takaran APC

Mutum 5 kacal ke neman takarar shugaban Najeriya tsakani da Allah inji ‘Dan takaran APC

  • Kayode Fayemi ya ziyarci jihar Neja da nufin samun kuri’un ‘ya 'ya yan APC a zaben fitar da gwani
  • Fayemi ya zargi wasu ‘yan takarar da cewa sun cika wuri ne kurum, amma ba da gaske suke yi ba
  • Gwamnan na Ekiti yana neman APC ta tsaida shi a matsayin ‘dan takarar shugaban kasa a 2023

Niger - Mai girma gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi ya zargi wasu masu neman shugabancin Najeriya da cewa ba da gaske suka shiga takaran ba.

Jaridar Premium Times ta ce ‘dan takarar shugaban kasar na APC ya yi wannan magana ne yayin da ya ziyarci ‘yan jam’iyya a garin Minna, jihar Neja.

Gwamna Kayode Fayemi ya ce cikin mutum 23 da ke neman tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a APC, kusan biyar ne kawai su ka shirya da gaske.

Kara karanta wannan

Zulum: Allah ke ba da mulki, ba zan roki wani ya dauke ni abokin takarar shugaban kasa ba

Legit.ng Hausa ta fahimci Gwamnan bai kama sunan wadanda yake ganin da gaske suke takarar ba. Sai dai yanzu har wasu sun janye duk da sun saye fam.

Fayemi ya je jihar ta Neja ne a ranar Lahadi, 22 ga watan Mayu 2022, domin samun goyon bayan ‘yan APC a zaben fitar da gwani da za a yi a watan nan.

A jawabin da Femi Ige ya fitar, an ji ‘dan takarar yana cewa ana gane ‘dan takara da gaske yake yi ne ta hanyar wuraren da ya ziyarta, yana neman kuri’u.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kayode Fayemi a Minna Hoto: @kfayemi
Gwamna Kayode Fayemi a Minna Hoto: @kfayemi
Asali: Twitter

Femi Ige shi ne Mai magana da yawun bakin kwamitin yakin neman takarar Kayode Fayemi.

Zan kawo gyara - Fayemi

Kamar yadda This Day ta fitar da rahoto, Dr. Fayemi ya yi alkawarin kawo zaman lafiya a jihohin Najeriya, tare da kawo karshen sha’anin rashin wutar lantarki.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu ya bayyana irin yadda yake matukar son gaje Buhari, ya ce ba wasa yake ba

“Mutanen Najeriya ba su farin ciki da mu domin mun gagara kokarin ganin ana samun wutar lantarkin da bai daukewa.”
“Da zarar mun shawo kan kalubalen lantarki, to mun magance matsalar da kamfanoni su ke fama da shi wajen aiki da kyau.”

- Dr. Kayode John Fayemi

Da zan iya ... - Bello

Da yake jawabi, Gwamnan Neja, Abubakar Sani Bello ya ce da zai iya nada shugaban kasa, da Kayode Fayemi ne zai karbi mulki a shekara mai zuwa.

Gwamna Abubakar Sani Bello ya ce tun kafin Fayemi ya zo neman kuri’ar ‘yan jam’iyyar APC a zaben tsaida gwani, Gwamnan na Ekiti mutumin Neja ne.

Kwamiti ya hana Otu takara

A jiya aka ji labari rashin takardun firamare da WASC sun jawo Bassey Edet Otu ba zai nemi kujerar Gwamna a 2023 a Jam’iyyar APC a Kuros Ribas ba.

Sanata Bassey Edet Otu ya wakilci mazabun Calabar/Odukpani a Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa tun daga shekarar 2003 zuwa 2015 a karkashin PDP

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi alkawarin ba Shugaban Majalisa goyon bayan samun tikitin Shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel