Jerin Gwamnonin jihohi 17 da za su sauka daga kan kujerar mulki nan da watanni 12

Jerin Gwamnonin jihohi 17 da za su sauka daga kan kujerar mulki nan da watanni 12

  • Akwai Gwamnonin Najeriya masu-ci 17 da za su fita daga gidan gwamnati nan da shekara daya
  • Wasu daga cikin wadannan Gwamnoni sun kammala lissafin yadda za su tare a majalisar dattawa
  • Gwamnonin na PDP da na APC masu barin mulki za su nemi kujerar shugabancin Najeriya a 2023

Gwamnoni akalla 17 ne za su sauka daga kujerar da suke kai a Mayun 2023. A lokacin ne gwamnonin za su cika shekaru takwas su na kan mulki.

Daily Trust ta ce wasu daga cikin shugabannin nan sun ayyana wadanda suke so su gaje su. Dukkaninsu su na mulki ne karkashin APC da kuma PDP.

A jihohi 29 ne hukumar INEC za ta gudanar da zaben gwamnonin jihohi a shekara mai zuwa.

Daga cikin wadannan jihohi akwai 17 inda sabon gwamna za a tsaida. Ragowar duk za su nemi tazarce domin shekaru uku da suka wuce suka shiga ofis.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP ta fitar da duk wadanda za su yi mata takaran zaben 2023 a jihar Kano

An samu sama da mutane 20 da suka sayen fam din neman takarar gwamna a jam’iyyar APC. A bangare guda kuma, PDP mai hamayya ta saida fam 145.

Sauran jihohin su na yin na su zaben ne a lokaci dabam a dalilin shari’a a kotu. Wadannan jihohi sun hada da Bayelsa, Kogi, Edo, Osun, Ondo da sauransu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnonin jihohi
Gwamnonin Ekiti, Kebbi da Kogi Hoto: nairametrics.com
Asali: UGC

Gwamnonin da wa’adinsu zai kare a 2023

1. Okezie Ikpeazu (Abia)

2. Emmanuel Udom (Akwa Ibom)

3. Samuel Ortom (Benuwai)

4. Farfesa Ben Ayade (Kuros Riba)

5. Sanata Ifeanyi Okowa (Delta)

6. Dave Umahi (Ebonyi)

7. Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)

8. Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa)

9. Nasir El-Rufai (Kaduna)

10. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)

Har ila yau akwai

11. Aminu Bello Masari (Katsina)

12. Atiku Bagudu (Kebbi)

13. Abubakar Sani Bello (Niger)

14. Simon Lalong (Filato)

15. Nyesom Wike (Ribas)

16. Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto)

17. Darius Ishaku (Taraba)

Kara karanta wannan

Jam’iyyar APC ta jero sharudan da za su sa a hana mutum takara a 2023 bayan ya saye fam

Legit.ng Hausa ta fahimci Gwamnonin da za su nemi tazarce su 11 ne. Sun hada da: Ahmadu Fintiri, Bala Mohammed, Babagana Zulum, da Inuwa Yahaya.

Gwamnonin da suka ci buri

Ku na da labari Gwamnonin Benuwai, Filato, Neja, Kano da na Taraba za su nemi takarar Sanata. Wasu daga cikin gwamnonin su na neman shugaban kasa.

Gwamnan Filato, Simon Bako Lalong shi ne gwamnan da ya fara sayen fam din Sanata. A Neja ma an ji za a a fafata tsakanin Gwamna da Aliyu Sabi a APC.

Masu harin Aso Villa su ne; Badaru Abubakar, David Umahi da Ben Ayade a APC, sai Udom Emmanuel, Aminu Tambuwal, da kuma Nyesome Wike a PDP.

Asali: Legit.ng

Online view pixel