Shugaban kamfanin buga kudi ya ajiye aiki, ya shiga neman takara gadan-gadan a APC

Shugaban kamfanin buga kudi ya ajiye aiki, ya shiga neman takara gadan-gadan a APC

  • Abbas Umar Masanawa ya sauka daga kujerar da yake kai na shugaban Nigeria Security & Minting
  • Alhaji Abbas Umar Masanawa ya bi umarnin da shugaban kasa ya bada, zai nemi Gwamna Katsina
  • Masanawa zai gwabza da Mannir Yakubu, Mustapha Inuwa, Ahmad Kangiwa, da Dikko Radda a APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Tsohon shugaban kamfanin Nigeria Security and Minting masu buga kudin Najeriya, Abbas Umar Masanawa, zai yi takarar gwamna a Katsina.

Jaridar Leadership ta rahoto Abbas Umar Masanawa yana cewa ya bi umarnin da shugaban kasa ya bada ga masu neman takara da su sauka daga kujerunsu.

Da yake amsa tambaya daga ‘yan jarida a Abuja, Alhaji Abbas Umar Masanawa ya tabbatar da cewa zai yi takarar gwamnan jihar Katsina a zabe mai zuwa.

“Na yi murabus daga mukamina na Babban Manaja kuma Shugaban kamfanin Nigeria Security, Printing and Minting.”

Kara karanta wannan

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

“Na aika da takardar murabus dina ga shugaban majalisar da ke sa ido a kan kamfanin, wanda shi ne gwamnan CBN.”

- Abbas Umar Masanawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Nasarorin da Masanawa ya samu a ofis

The Cable ta ce Masanawa ya jero wasu daga cikin nasarorin da ya samu da yake rike da kamfanin.

Shugaban kamfanin buga kudi
Abbas Umar Masanawa ya saye fam a APC Hoto: www.sunnewsonline.com
Asali: UGC

A lokacinsa ne aka tada wasu matattun kamfanonin biga kudi, sannan ya yi kokari wajen ganin yanzu an daina shigo da kudin Najeriya daga kasashen ketare.

Kafin Masanawa ya shiga ofis, ya yi ikirarin kamfanin yana tafka asara, amma yanzu baya ga buga kudi da ake yi a gida, ana cin riba, kuma ana kula da albashi.

Tuni dai kwamitin APC ta tantance Abbas Masanawa a cikin masu neman takarar gwamnan jihar Katsina, kuma ya iya yi masu bayanin nasarorin da ya samu.

Kara karanta wannan

Yadda Jam’iyyar APC ta samu tayi wa Yari, Marafa da Gwamna Matawalle sulhu a Zamfara

Late comer ya shigo APC

Legit.ng Hausa ta na da labari an fara labarin takarar Alhaji Abbas Masanawa a jihar Katsina, an fara maganar ya samu tikitin APC, ya kuma lashe babban zabe.

Masanawa ya shigo takarar ne a lokacin da aka rasa wanda zai yi nasara a zaben gwanin jam’iyyar APC tsakanin wadanda suka yanke tikiti tun tuni a APC.

Masu neman tuta a jam’iyya mai mulki sun hada da Mannir Yakubu, Mustapha Inuwa, Arch. Ahmad Kangiwa, Dr. Dikko Radda sai Alhaji Farouk Lawal Jobe.

Ahmed Musa Dangiwa ya shigo takara

A watan Afrilu aka ji labari Ahmed Musa Dangiwa ya kammala wa'adinsa a matsayin shugaban bankin nan na FMBN a Najeriya, ya shiga takarar gwamna a APC.

Ahmed Musa Dangiwa zai fuskanci mataimakin gwamna mai-ci, da tsohon sakataren gwamnatin Katsina da Masanawa wajen samun tikitin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel