Tsohon Shugaba Obasanjo ya fadawa ‘Dan takaran PDP sirrin yadda za a gyara Najeriya

Tsohon Shugaba Obasanjo ya fadawa ‘Dan takaran PDP sirrin yadda za a gyara Najeriya

  • Olusegun Obasanjo ya zauna da Mohammed Hayatu-Deen mai neman tikitin shugaban kasa a PDP
  • Tsohon shugaban kasar ya ce abubuwa sun jagwalgwale a yau, ya yi bayanin yadda za a kawo gyara
  • Obasanjo ya ce gyara Najeriya a yanzu na bukatar ilmi, hangen nesa, dabaru da mahaukacin kishi

Ogun - Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce al'umma su na bukatar shugaba ne wanda ke kaunar kasar nan domin abubuwa su gyaru.

The Cable ta ce a ranar Alhamis 19 ga watan Mayu 2022, Olusegun Obasanjo ya hadu da Mohammed Hayatu-Deen mai neman yin takara a PDP.

Mohammed Hayatu-Deen wanda tsohon shugaban bankin nan na FSB International Bank ya hadu da tsohon shugaban kasar a gidansa a jihar Ogun.

Olusegun Obasanjo ya shaidawa Hayatu-Deen cewa abubuwa sun tabarbarewa kowa a Najeriya, amma ya ce duk da haka za a iya shawo kan matsalolin.

Kara karanta wannan

Saraki ya bayyana ainahin abun da ya haddasa rashin tsaro a Najeriya

Obasanjo wanda ya yi mulki sau biyu ya ce yanzu an daina maganar Najeriya a taron Duniya.

Vanguard ta ce tsohon shugaban kasar ya jero wasu abubuwa da ake bukata idan ana so a samu cigaba. Daga ciki shi ne a samu wanda zai haukacewa kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon Shugaba Obasanjo
Obasanjo ya zauna da Mohammed Hayatu-deen Hoto: www.today.ng
Asali: UGC

Jawabin Olusegun Obasanjo

“Zan yi tunanin abubuwa hudu – na daya shi ne ilmi. Idan ba a damawa da Najeriya, kila ilmin da ya kamata mu samu a kan kanmu da yankinmu ya yi karanci ne.”
“Na biyu shi ne hangen nesa. Wani hangen nesa mu ke da shi? Idan ba ka da hangen nesa, ka zama makaho, duk da watakila ka na da idanu. Halin da mu ke ciki kenan.”
“Na uku shi ne sha’awa. Ina fadawa mutane da safiyar nan cewa sha’awa na nufin hauka – dole ka haukace a game da kishin Najeriya. Ba na neman afuwa kan hakan.”

Kara karanta wannan

Matasa sun nuna fushinsu yayin da wata Naomi Goni ta kara ɓatanci ga Annabi SAW, an kama 3

- Olusegun Obasanjo

A cewar Obasanjo, ya haukace a game da Najeriya domin bai da wata kasa sai ita a Duniya.

"Na hudu shi ne tunani. Ba zai yiwu a cigaba da yin abubuwan da ba su aiki ba, kuma a sa ran za a ga canji. Dole mu kirkiro wasu abubuwan, sai mun canza dabara.”

- Olusegun Obasanjo

2023: Amaechi ne ya dace - Buratai

Ku na da labari cewa Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana dalilin da ya sa yake goyon bayan Rotimi Amaechi ya zama shugaban kasa bayan Muhammadu Buhari.

Tukur Buratai yana ganin tsohon Ministan sufurin ya fi dacewa ya karbi shugabanci a zaben 2023 saboda ya yi abin a yaba a duk mukaman da ya rike daga 1999 zuwa yau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng