Labari ya canza bayan Ganduje ya hakura da neman takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a 2023

Labari ya canza bayan Ganduje ya hakura da neman takarar ‘Dan Majalisar Dattawa a 2023

  • Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba zai nemi kujerar Majalisar Dattawa a Kano a zabe mai zuwa ba
  • Dr. Abdullahi Ganduje ya hakura Barau Ibrahim Jibrin ya sake yin takara a jam’iyyar APC mai mulki
  • Babu mamaki Sanata mai-ci, Barau Jibrin zai kara da jam’iyyun PDP da NNPP a APC mai mulki

Kano - Alamu su na nuna cewa Mai girma gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya hakura da neman kujerar Sanata a zabe mai zuwa.

Jaridar Leadership Hausa ta fitar da rahoto a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu 2022 da ya bayyana cewa Abdullahi Umar Ganduje ya fasa yin takaran.

Gwamnan ya dauki wannan matsaya ne a sakamakon sasantawa da aka yi tsakanin bangarensa a APC da kuma tsagin Sanata Barau Ibrahim Jibrin.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

A karshen zaman sulhun da aka yi a daren yau, Abdullahi Umar Ganduje ya hakura da zuwa majalisa, ya kyale Jibrin ya sake neman kujerarsa.

Kamar yadda mu ka samu rahoto, an yi wannan zama na ranar Lahadi ne a birnin tarayya Abuja.

Shekarau ya fita, Barau ya zauna

Yayin da kafar Sanatan Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau ta fara barin APC, Barau Ibrahim Jibrin ya yi zamansa a jam’iyya mai mulki.

Sanata Barau Ibrahim Jibrin da Ibrahim Shekarau su na cikin jagororin tafiyar G7, wanda ta ke adawa da shugabancin Abdullahi Abbas a jihar Kano.

Ganin jam’iyyar NNPP da Sanata Rabiu Kwankwaso tayi nisa wajen zawarcin tsohon gwamna Shekarau, watakila shiyasa aka yi sulhu da su Jibrin.

Ahmed Prince Gandujiyya, daya daga cikin magoya bayan ‘dan majalisar, ya tabbatar da wannan labari da yake magana a shafin Facebook yau da safe.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Ganduje
Gwamnan Kano Ganduje tare da manyan APC Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

Shi ma Abubakar Aminu Ibrahim wanda Hadimi ne wajen Gwamnan Kano, ya nuna labarin ya tabbata, ya daura hoton da ke nuna Ganduje ya hakura.

Jibrin zai koma karo na uku?

Tun a zaben 2015 dai Barau Ibrahim Jibrin ya zama Sanatan Arewacin jihar Kano a karkashin APC. A zaben 2019 ne ya zarce a kan wannan kujerar.

Yayin da zaben 2023 ya karaso, sai ‘dan majalisar ya nuna sha’awar ya zama Gwamnan jihar Kano. A karshe dai suka yi ta rikici har aka je gaban kotu.

Maliya ya sha da kyar a APC?

Bayan bangaren G7 ya rasa kara a kotun koli, an ji labari Jibrin ya saye fam din Sanata domin ya koma majalisa bayan an ayyana Nasiru Gawuna a APC.

Bayan nan sai aka ji Abdullahi Ganduje ya saye fam din shiga zaben takarar ‘dan majalisar dattawa a 2023, yana hangen kujerar da Jibrin yake kai.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel