Ministan Albarkatun Man Fetur, Timpre Sylva, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023

Ministan Albarkatun Man Fetur, Timpre Sylva, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023

  • Karamin ministan man fetur, Timipre Sylva, ya janye daga takarar shugaban kasa ya koma bakin aiki
  • Wata majiya daga ma'aikatar ta bayyana cewa ministan ya ɗauki matakin domin taimaka wa shugaba Buhari ya karasa wa'adinsa
  • Babban mai taimaka wa ministan kan harkokin midiya, Horatious Egua, ya tabbatar da cewa Uban gidansa ya koma aiki

Abuja - Ƙaramin ministan Albarkatun man Fetur, Chief Timipre Sylva, ya janye daga takarar shugaban ƙasa karkashin APC ya koma bakin aiki, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Idan baku mance ba a ranar 9 ga watan Mayu, wata ƙungiyar arewa ta lale kuɗi ta sayi Fam, ta gabatar masa domin ba shi damar shiga a fafata da shi a zaɓen fidda gwanin APC.

Kara karanta wannan

Sokoto: Wani Malami ya yi alkawarin daukar nauyin iyayen ɗalibar da ta zagi Annabi, yace sun gama wahala a duniya

Ministan Albarkatun Man Fetur, Timpre Sylva.
Ministan Albarkatun Man Fetur, Timpre Sylva, ya janye daga takarar shugaban ƙasa a 2023 Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Wani ma'aikaci a ma'aikatar Man Fetur, wanda ya nemi a ɓoye sunansa yace Sylva ya janye daga takarar shugaban ƙasa don samun damar taimaka wa shugaba Buhari ya cika kyawawan kudirorinsa.

Ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Dama ya yi alƙawarin neman shawarin jagororin ƙasar nan da shugabannin na siyasa tun ranar da aka gabatar masa da Fom. Ya yi amanna cewa cigaba da aikinsa zai ƙara jawo wa Najeriya zuba hannun jari da yawa."
"Yayin da ya yi shawara ya gane cewa kalubalen da ke ɓangaren Man Fetur sun isa ya fara kokarin nemo hanyoyin warware su fiye da ya tafi neman kujerar shugaban ƙasa."
"Ɓangaren albarkatun mai ne ginshikin zaman lafiyar tattalin arzikin ƙasar nan kuma ba ma'aikata ba ce da wani zai zo lokaci guda ya cigaba da tafiyad da ita. Akwai bukatar lokaci ka fahimci tsarin."

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Meyasa ya jingine takara?

Majiya ta ƙara da cewa bayan dogon nazari ministan ya yanke shawarar jingine batun takara saboda ya cigaba da ba da gudummuwa a ragowar wa'adin gwamnatin Buhari.

Babban mai taimakawa Ministan kan harkokin midiya, Ministan Horatious Egua, ya tabbatar wa NAN cewa Ministan ya koma bakin aiki.

A wani labarin na daban kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel