Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

  • Alhaji Atiku Abubakar ya yi alkawarin yaki da rashawa idan ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa
  • Atiku ya daurawa gwamnatin APC nauyin yajin aikin da kungiyar malaman jami'a ASUU ke ciki
  • ASUU ta kwashe kimanin watanni hudu yanzu a yajin aiki kuma ta tsawaita da watanni uku

Rivers - Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin Peoples’ Democratic Party PDP, Atiku Abubakar, ya rantse da Allah cewa zai tabbatar da cewa babu wanda yayi sata idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Hakazalika ya yi alkawarin cewa zai mayar da hankali kan lamarin ilmi kuma ya kawo karshen yajin aikin da Lakcarori ke yi.

Atiku ya bayyana hakan ne yayinda ya kai ziyara jihar Rivers don tattaunawa da Deleget din jihar a birnin Fatakwal, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Masu cewa ba ni da isasshen lafiya basu da hankali, mahaukata ne: Tinubu

Atiku
Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku Hoto: Atiku
Asali: Twitter

Atiku ya bayyana bacin ransa kan yadda dubunnan dalibai ke zaune a gida saboda gwamnatin APC ta sace kudin da ya kamata ace anyi amfani da su wajen gyara sashen Ilmi.

Yace:

"Zan tabbatar da cewa an sa ido sashen Ilimi. A yau an kulle dukkan jami'o'i tsawon watanni yanzu. Saboda suna sace kudin. Zan tabbatar da cewa babu wanda zai sace kudi, na ranste."

Tsohon mataimakin shugaban kasa yace gwamnatin APC ta raba kawunan yan Najeriya kuma ta tsananta matsalar tsaro.

Atiku na neman kuri'u, ya bayyana manyan manufofinsa guda biyar kwarara

Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma mai neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, a ranar Lahadi, ya ce yana da wasu manufofin ci gaba guda biyar da ya tanadarwa kasar idan ya zama shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Daliban kwalejin ilimin Shehu Shagari sun kashe daliba kan zargin batanci ga Annabi

Atiku wanda ya gana da wakilan PDP na jihar Abia a babban taron jam’iyyar na kasa a dakin taro na gidan gwamnati, ya lissafa manufofinsa na ci gaba guda biyar da suka hada da; hada kai, magance matsalar rashin tsaro, tattalin arziki, ilimi, da sake fasalin kasa.

Ya bayyana cewa kudu maso yamma shi ne ainihin inda ya sa a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel