Rikicin siyasar Kano: A yau Shekarau zai fice daga APC, zai hade da Kwankwaso

Rikicin siyasar Kano: A yau Shekarau zai fice daga APC, zai hade da Kwankwaso

  • Alamu sun gama tabbatar da cewa, a yau ne tsohon gwamnan Kano Shekarau zai koma jam'iyyar NNPP mai tasowa
  • Wannan na zuwa ne bayan da tashin-tashina ta barke a siyasar Kano musamman a jam'iyya mai ci ta APC
  • A halin da ake ciki, ana ta shirye-shiryen yadda tsohon gwamnan zai zama mamban NNPP, inda za su jame da Kwankwaso

Jihar Kano - A yau ne tsohon gwamnan jihar Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau zai bayyana ficewarsa daga jam'iyyar APC mai mulki.

Shekarau, wanda ke jagorantar bangaren G-7 na APC a Kano, ya samu sabani da Gwamna Ganduje, duk da cewa hukuncin da kotun koli ta yanke a makon da ya wuce ya kawo karshen kungiyar G-7, inda a karshe aka mika ragamar shugabancin jam’iyyar ga tsagin gwamnan.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Dan majalisa da shugaban karamar hukuma a Kano sun fasa shiga NNPP

Wasu jiga-jigan APC da dama sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NNPP karkashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Daily Trust ta ruwaito.

Shekarau zai koma NNPP yau Litinin
Rikicin APC a Kano: Shekarau zai fice daga jam'iyyar APC ya hada kai da Kwankwaso | Hoto: dailynigerian.com
Asali: Twitter

A ranar Asabar ne kuma ake sa ran Shekarau zai bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a hukumance amma shirin ya ci tura saboda wani dalili da ba a bayyana ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yayin da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC ke shelanta sauya sheka zuwa NNPP a ranar Juma’a, Ganduje ya ziyarci Shekarau da daddare domin dakile sauya shekarsa daga bisani kuma aka kira su biyun zuwa Abuja.

Sai dai Malam Shekarau ya yi watsi da ganawar ta Abuja bayan da aka ce ya tattaro cewa ba fadar shugaban kasa ce ta kira zaman sulhun ba.

Bayan ziyarar ta Ganduje, tawagar ta Kwankwaso sun ziyarci Shekarau domin tabbatar da cewa shirin sauya shekarsa na nan daram.

Kara karanta wannan

Siyasar Kano: Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

Sai dai babu wata masaniya daga sansanin Shekarau kan dalilin sauya shekar.

An tattaro cewa, cewa Shekarau bai ji dadin martanin da magoya bayansa suka yi wa Ganduje a ranar Juma’a ba, kasancewar an yiwa gwamnan ihu lokacin da ya isa gidan Shekarau a Mudunbawa Kano.

Yunkurin Tinubu na hana batun sauya shekar Shekarau

Daily Trust ta kara da cewa Shekarau ya tafi Abuja ne a ranar Asabar din da ta gabata bisa gayyatar jagoran jam’iyyar APC na kasa da kuma dan takarar shugaban kasa a 2023 a dandalin jam’iyyar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da aka kasa tantance sakamakon ganawar, wacce ta dauki tsawon sa’o’i da dama, majiyoyi daga tsagin Malam Shekarau na nuni da cewa ganawar bata dakile batun shirin sauya shekar Shekarau ba.

Hakazalika, an tattaro cewa a yammacin ranar Asabar ne shugabannin APC na Kano suka aika foma-foman majalisar wakilai ta kasa guda biyar da na jiha biyu ga Shekarau.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

Duk da haka, majalisar shura, wadda ita ce mafi girma wajen yanke shawara a sansanin Shekarau ta ki amincewa da ba da bakin.

Daya daga cikin majiyar ta kara da cewa Malam Shekarau ya koma Kano da safiyar jiya Lahadi inda ya umurci kowa da kowa ya shirya tsaf domin tunkarar sabuwar tafiyar da zai fara yau Litinin.

Kwankwaso ya nemi tabbacin karshe daga Shekarau

Bayan ‘yan sa’o’i da dawowar Shekarau, Kwankwaso ya garzaya gidansa don kammala yarjejeniyarsu ta sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP.

Ba a iya tantance sakamakon ganawar ba, sai dai majiyoyi sun shaida cewa sauya shekar na nan, domin dukkan na hannun daman tsohon gwamnan a dukkanin kananan hukumomi 44 na jihar sun amince ya koma NNPP.

Siyasar Kano: Dan majalisa da shugaban karamar hukuma a Kano sun fasa shiga NNPP

A wani labarin, Murtala Kore, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dambatta a majalisar dokokin Kano, ya fasa sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP ta su sanata Kwankwaso.

Kara karanta wannan

Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan APC sun dira filin Malam Aminu Kano

Haka kuma, shugaban karamar hukumar Dambatta, Mohammed Kore, ya janye shawararsa na komawa jam’iyyar ta NNPP.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ‘yan siyasan biyu sun sanar da sauya sheka zuwa NNPP tare da shugaban ma’aikatan gwamna Ganduje, Ali Makoda a ranar Alhamis din da ta gabata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel