Siyasar Kano: Dan majalisa da shugaban karamar hukuma a Kano sun fasa shiga NNPP

Siyasar Kano: Dan majalisa da shugaban karamar hukuma a Kano sun fasa shiga NNPP

  • Ana ci gaba da kai ruwa rana a siyasar jihar Kano, wasu jiga-jigan APC na jihar sun yi amai sun lashe a yanzu
  • Dan majalisa a Kano tare da shugaban karamar hukuma sun magantu kan yiwuwar komawarsu jam'iyyar NNPP
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan da suka ce sun bar APC mai mulki da kuma tsagin gwamna Ganduje

Kano - Murtala Kore, dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Dambatta a majalisar dokokin Kano, ya fasa sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa NNPP ta su sanata Kwankwaso.

Haka kuma, shugaban karamar hukumar Dambatta, Mohammed Kore, ya janye shawararsa na komawa jam’iyyar ta NNPP.

Wainar da ake toyawa a siyasar Kano
Dan majalisa da shugaban karamar hukuma a Kano sun fasa shiga NNPP | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, ‘yan siyasan biyu sun sanar da sauya sheka zuwa NNPP tare da shugaban ma’aikatan gwamna Ganduje, Ali Makoda a ranar Alhamis din da ta gabata.

Kara karanta wannan

Kano: Shugaban Ma'aikatan Fadar Ganduje, Shugaban Karamar Hukuma, Ƴan Majalisa 2, Auditan APC Da Shugaban Matasa Duk Sun Koma NNPP

Sai dai an ji su biyun a wani faifan bidiyo a ranar Lahadi, inda suka janye matsayarsu na komawa NNPP, suna masu cewa "har yanzu muna APC".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dan majalisar ya ce:

“Ina son sanar da jama’a cewa har yanzu ina nan a APC, jam’iyyar Baba Ganduje, Buhari, Nasiru Gawuna, Murtala Sule Garo da sauran masu ruwa da tsaki.
“Duk da wata ‘yar karamar matsala da ta faru kimanin kwanaki uku da suka gabata, ina so in mayar da biyayyata ga APC. Mun yanke hukuncin da bai dace ba cikin gaggawa amma yanzu an sasanta lamarin cikin ruwan sanyi.
“Har yanzu ina nan a jam’iyyar APC kuma ina kira ga kowane dan jam’iyyar APC a karamar hukumar Dambatta da ya fito ya bayar da gudunmawa mai tsoka domin samun nasarar jam’iyyar a 2023 a dukkan matakai.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ganduje Ya Dira Gidan Shekarau 'Don Ƙoƙarin Hana Shi Fita Daga APC'

“Ina neman afuwar kowa da kowa game da abin da ya faru. Ina tabbatar muku cewa komai ya warwaru yanzu.”

A nasa bangaren, Shugaban karamar hukumar Dambatta ya ce:

“Ni tare da mataimakina Hamisu Magaji Galadima, ina so in sanar da cewa ba mu sauya sheka zuwa NNPP ba. Har yanzu muna APC.
“Za mu ci gaba da kasancewa a jam’iyyar kuma mu tabbatar ta lashe zaben 2023 a dukkan matakai.
“Mu ‘yan jam’iyyar APC ne kuma muna ci gaba da kasancewa a cikinta. Abin da ya faru kimanin kwanaki uku da suka wuce ba shawara bace mai kyau amma yanzu mun koma gidanmu na gaske.
“Mun yi alkawarin yin biyayya ga mai girma Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da dan takararmu, Nasiru Yusuf Gawuna da abokin takararsa, Murtala Sule Garo."

Ganduje bai sani yin takarar sanatan Kano ta tsakiya ba, yin kaina ne - Lado

Tsohon sanata mai wakiltan yankin Kano ta tsakiya, Sanata Basheer Garba Mohammed (Lado), ya bayyana cewa ba za a iya yi masa makarkashiya don lalata kudirinsa na komawa majalisar dattawa ba a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

A cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Asabar, Sanata Lado ya nesanta kansa daga rahoton kwanan nan kan wani furuci da aka alakanta da tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Malam Ibrahim Shekarau, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce:

“Na yi matukar damuwa da karanta wani labari a shafukan politicsdigest.ng da alfijir.com.ng a ranar 9 ga watan Mayun 2022 da wasu kafofin watsa labarai da dama, wanda ya nakalto Malam Ibrahim Shekarau yana cewa Mai Girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya umurce ni da na yi takarar kujerar sanata mai wakiltan Kano ta tsakiya."

Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa

A wani labarin, tsohon ministan harkokin Neje Delta, Sanata Godwill Akpabio, ya ce bai janye daga tseren takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, a ranar Lahadi, Akpabio ya ce jita-jitan da ke yawo na cewa ya hakura da takarar kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari abun dariya ne.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisar Kano da Kwamishinan Ganduje, za su bi Kwankwaso zuwa Jam’iyyar NNPP

Tsohon ministan ya jadadda cewa yana nan daram-dam a cikin tseren, yana mai cewa zai lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel