Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa

Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa

  • Sanata Godswill Akpabio ya yi martani kan jita-jitan da ke yawo cewa ya janye daga tseren kujerar shugaban kasar
  • Akpabio ya bayyana ikirarin a matsayin abun dariya, yana mai cewa har yanzu yana ta cikin masu so su gaji shugaba Buhari a 2023
  • Akpabio ya nuna karfin gwiwar cewa zai lashe tikitin shugaban kasa na APC dama na babban zaben mai zuwa

AbujaTsohon ministan harkokin Neje Delta, Sanata Godwill Akpabio, ya ce bai janye daga tseren takarar kujerar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ba.

A cikin wata wallafa da ya yi a shafinsa na Facebook, a ranar Lahadi, Akpabio ya ce jita-jitan da ke yawo na cewa ya hakura da takarar kujerar shugaban kasa Muhammadu Buhari abun dariya ne.

Tsohon ministan ya jadadda cewa yana nan daram-dam a cikin tseren, yana mai cewa zai lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m

Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa
Tsohon ministan Buhari ya magantu kan rade-radin janyewa daga tseren shugaban kasa Hoto: Godswill Obot Akpabio
Asali: Facebook

Hakazalika, ya bayyana cewa rahotanni da ke yawo cewa ya yanki fom din takarar kujerar sanata kanzon kurege ne.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewar zai yi nasara a babban zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023.

Ya ce:

“Jita-jitan da ke yawo cewa na janye daga tseren kujerar shugaban kasa abun dariya ne ko shakka babu.
“Ban janye ba, haka kuma ban yanki kowani fom din takarar sanata ba, kamar yawwa wata jarida ta wallafa a yau.
“Har yanzu ina cikin tseren kuma ina ciki don yin nasara. Jita-jitan janyewata alamu ne na cewa ana tsoron kasancewar mutum irina a tseren.
“Ban janye ba, b azan janye ba. Zan lashe wannan tseren kuma za a rantsar da ni a matsayin shugaban kasarku na gaba da izinin Allah a 2023.”

Mai neman takarar shugaban kasa a APC ya bayyana gaban kwamitin tantance sanatoci bayan ya siya fom din N100m

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilin da yasa Buhari ba zai binciki wadanda ke siyan fom din miliyan N100 ba

A wani labarin, mun ji cewa an tantance tsohon shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, domin takarar kujerar sanata a karkashin jam’iyyar mai mulki.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Oshiomhole ya bayyana a gaban kwamitin tantancewar duk da cewar ya biya naira miliyan 100 na fom din shugaban kasa tare da kaddamar da kamfen dinsa na shugaban kasa.

An tattaro cewa tsohon gwamnan na jihar Edo ya isa wajen tantancewar da ke Fraiser Suite, Abuja, da misalin karfe 8:12 na dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel